Tafarnuwa tana daga cikin tsirrai mafiya amfani waɗanda duniya ta dade tana amfana dasu wajen magance cututtuka da dama dake addabar ɗan Adam.
Ga wasu kadan daga cikin fa’idodin da take dauke dasu kamar yadda bincike ya tabbatar.
- CIWON DAJI (CANCER)
Duk mutumin da yake fama da ciwon daji ya yawaita amfani da tafarnuwa. Insha Allah zai samu waraka.
Idan ciwon Cancer din akan fatar jiki ne, sai ya rika shafawa ajikinsa bayan yasha cokali guda tare da zuma.
Idan kuma sankaran mama ne (Breast Cancer) wanda mata suke fama dashi, to duk matar da take fama da wannan ciwon sai ta rinƙa yawan yin girki da tafarnuwa (kamar Jollof rice, ko Pepper Soup, da sauransu). Sannan ta rika shan tafarnuwar wacce aka gauraya tare da Man habbah, kuma tana shafawa ajikin maman (nono). Insha Allah zata warke,
- BASUR ƊAN KANOMA
Duk wanda basur yake damunsa, ko yana shan wahala wajen fitar bayan gida, ko kuma masu yin bayan gida da jini, ko masu fama da kumburin ciki, ko kaikayin dubura, ga wani albishir gareku
Kuje ku samo tafarnuwa mai kyau. (kamar guda biyu ko uku manya) sai ku cire bawon sannan ku bayar a daka maku fura da ita.
Ku sami nono mai kyau kunashan wannan furar dashi. Insha Allahu awannan ranar ko washegari duk zaku fitar da basur din dake cikinku sannan zaku sami lafiya daga cutar basur da Izinin Allah
Sannan kuma sai kuna rinƙa gauraya Man Tafarnuwa tare da zuma kana shan cikin babban cokali biyu kullum daya da safe daya da dare. Insha Allah ku da basur kunyi sallama.
- SANYI MAI KUMBURIN JIKI
Duk mutumin da sanyi ya kumburashi, ko kuma sanyin ya ratsashi, kullum hancinsa ba ya rabuwa da majina, shima ga albishir
Ka samo ganyen Na’a-Na’a ka tafasa tare da citta (ginger) sannan ka zuba man tafarnuwa cikin babban cokali guda aciki. ka sanya zuma cokali ɗaya sannan kasha.
Haka zaka rinƙa yi har sati guda zuwa kwanaki 10. kuma kana iya shafa man tafarnuwar ajikinka In Allah ya yarda jikinka zai sabe, sanyin zai fita, kuma zaka warke sannan ka yiwa Allah ta’ala godiya,
- SANYIN ƘASHI
Masu fama da sanyin ƙashi ko kuma Rikewar gabobi (Arthritis) ga naku
kawai ku sami man tafarnuwa mai kyau, ku gaurayashi da man habbatus sauda, Sannan a dorashi bisa wuta mai ci ahanakali. Idan yayi kamar minti biyar sai a sauƙe.
Wannan man mai dumi za’a rika shafawa ajikin ƙafar, ko bayan, ko kwankwaso. Insha Allah ko da ciwon bayan yafi shekara goma ana fama, to za’a samu lafiya da izinin Allah,
- HAWAN JINI / CIWON ZUCIYA
Bincike ya tabbatar da cewa tafarnuwa tana narkar da mummunan kitsen nan na Cholesterol wanda shine yake toshe kofofin zuciyar Ɗan Adam, har ake samun hawan jini ko ciwon zuciya.
To tafarnuwa tana narkar dashi kuma tana buɗe duk hanyoyin da suka toshe. sannan tana tsaftace jinin jikin Ɗan Adam.
Ana so masu fama da hawan jini suyi wannan hadin domin samun kuzari da lafiya da ikon Allah:
Za’a samo ganyen zogale ɗanye a tafasa tare da tafarnuwa sai atace. Bayan an taceshi kafin asha sai a sanya Man Zaitun cikin babban cokali ɗaya, asanya zuma sannan anasha. Kuma ayawaita cin tafarnuwa acikin abinci yau da kullum. Insha Allah za’a dace,
- TYPHOID FEVER / TSUTSAR CIKI / ULCER
Duk masu fama da wannan larurar ga magani nan da yardar Allah : Ka riƙa shan cokali guda na tafarnuwa gauraye da zuma kullum da safe, minti 30 kafin breakfast.
Insha Allah wannan zai kashe duk kwayoyin cutar dake cikin cikinka. Hakanan masu macijin ciki ko tsutsar ciki suma tsotsotsin zasu mutu. kuma zasu fita da izinin Allah.
Hakanan masu fama da gyambon ciki (Ulcer) suma zasu samu saukinta idan suka bi wannan hanyar.amma masu Olsa sai sunci abinci sa’anan zasu sha wannan haɗin Kuma su rinƙa sanya cokali guda na man tafarnuwar acikin dukkan abincin da zasu ci. Ko kuma a rinƙa dafa abincin tare da ita,
- CIWON HANTA :
Tafarnuwa tana bama hantar Ɗan Adam kariya daga cutattuka. Kuma amfani da ita yana hana kitsen nan na cholesterol taruwa ko ginuwa ajikin hanta, ballantana har a samu matsalar ciwon ciki ko Kumburin Hanta.
Masu ciwon hanta su rika shan man tafarnuwa ko garinta wanda aka cakuda da zuma. Insha Allah Za’aga abun mamaki wato za’a sami lafiya cikin ƙanƙanin lokaci.
Daga Nasara Islamic Medicine Research Centre
Domin neman ƙarin bayani ko buƙatar magunguna
Email Address
Traditionalmedicinestore@gmail.com