Runduna Ta Uku Rundunar Zaidu Dan Harisatu Ya Jagoranta.

1 237

Get real time updates directly on you device, subscribe now.


Bayan Manzon ALLAH (SAW) yayi hijira daga Makka zuwa madina, Bayan wannan hijira ne kafirai suka ci gaba da azabtarwa da cutar da musulman da suke agarin Makkah harma daga karshe kafirai suka yiwa musulamai korar da ake yiwa kare suka fitar da musulmai daga cikin garin Makkah bayan sun kwace dokiyoyin su.

To akan haka ne sukuma musulmai suka yi niyar mayar da murtani akan wannan zalunci da aka yiwa yan uwan mu musulmai, ana cikin wannan yanayi ne kuwa sai labara ya zowa manzon {saw} cewa ga wasu ayarin kafirai can sun dawo daga fatauci daga kasar sham zuwa Makkah kuma suna dauke da kyawawan kalolin abinci tare da tsadadun riguna na alfahari, a lokacin babu abin da manzon ALLAH {saw} ya fara yi sai ya zabi wani gwarzo daga cikn jaruman barade daga cikin sahabbai wannan gwarzo, manzon ALLAH {saw} yana yawn shugabantar da shi a cikin mafiya yawan yake-yake.

Ita dai wannan runduna ta kafu ne acin shekara ta uku da yin hijirar manzon ALLAH {saw} daga makkah zuwa madina.

Manzon ALLAH {saw] ya gayawa Zaidu wannan fita da za aiyi kuma ya shugabanci zababbun sadaukaia cikin musulmai har sadaukai saba’in.

Kowane daga cikin sadukan nan sunyi alkawari tsakanin su da Allah zasu tsaya da kafafuwan su komai wahala komai runtsi komai azaba har sai sun kare tutar musulunci kuma tsananin yaki bazai sasu su juya ba, ita dai wannan rundun tafita daga cikin madina a karkashin jagorancin Zaidu Dan Sabitu tare da cewa sun sani akwai tafiya mai nisan gaske kafin su hadu da wadan can kafiran domin zasuyi tafiyar kwanaki kafin su hadu amma duk da haka basu damu ba suna tafiya wasu haye akan rakuma wasu kuma suna tafiya a kasa, sai da sukayi tafiyar kwana hudu dare da rana kowanensu yana mai jure wahalar tafiya amma basu damu ba, suna tafiya suna masu yin tasbihi tare da sauke farali na sallah a kowane lokaci, su sancewa wannan tafiya tasu Allah da Manzon su ne suka yi umarni kuma koda basuyi yaki cikin ta ba to sun sandai sun tafi abisa umarnin Allah tare da niyyar rusa barna da kuma kafirci a doran kasa.

To bayan wannan runduna ta musulunci ta isa wani guri da ake cewa Aisu, wanda yake yamma daga garin madina to anna ne wannan runduna ta hadu da wannan ayari na mushirikai batare da tsayawa komai ba nan take suka afka musu, suka ribace duk abin da suke dauke da shi na daga dukiyoyi masu yawa, Zinare da Azurfa, wanda mafi aksarin dukiyar ta wani mashahurin mushiriki ne kuma shugaba daga cikinsu, wato Safwanu Dan Umayyu Dan Halfa.

Musulmai sun kama wasu daga cikin wannan ayari da ga ciki akwai Abul’asi wanda ya auri Zainab yar Manzon ALLAH {saw} wanda a lokacin bai musulunta ba.

To a lokaci da wannan runduna ta musulunci ta kama hanyarta ta dawowa , suna tafiya idan lokacin sallah yayi su tsaya suyita acikin nutsuwa da tsoran Allah.

Ana cikin wannan hali ne sai shi wannan Abul’asi yayi tunani shifa yau gashi ankamo shi a matsayin fursunan yaki kuma matar da ya aura tana can wurin mahaifinta wato manzon ALLAH {saw} to yanzu mai yakamata da shi.

To kafin wannan yaki shi wannan mutum ya taba farantawa manzon ALLAH {saw} yayiwa manzon ALLAH {saw} alkawarin cewa zai aiko masa da yarsa wato zainab tunda shi bai musulunta ba, kuma yacika wannan alkawari ya aiko da ita a bisa zabin kansa, ta wannan abin ya farantawa Manzon ALLAH {saw} Duk da ta wahala kafin tazo madina domin wasu daga cikin kafirai sun hanata zuwa madina harma suka jawota daga kan rakumi ta fado wannan yazama sanadiyar zubewar cikinta.

To shi dai wannan sahabi Abul’asi yana zaune yana kallon musulmai suna sallah shi kuma sai ya yanke shawarar idan dare yayi ya sulale yaje ya buya a gidan Manzon ALLAH {saw} domin ya kama kafa da matar sa haka kuwa akayi, domin duhu yan bullowa sai Abul’asi ya sulale yakama hanya har ma ya riga musulmai shugowa garin madina, ya kai kansa wurin matar sa yace ki tseratar dani.

Ko shakka babu Nana Zainab tayi farin ciki da ganin wannan miji nata. To a lokacin da wannan abu ya faru daidai lokacin sallar asuba ne shikuma shugaban halite yana masallaci ne kafin a tashi sallah a inda wasu suke sallah wasu kuma na tasbihi wasu kuma karatun Alqur’ani har dai lokacin sallah yay Manzon ALLAH { saw } ya tashi ya fara sallah a cikin khushu’I da nutsuwa , tare da sahabbansa can sai aka ji wani sauti na Nana Zainab daga gidan Manzon ALLAH {saw} tana cewa.

“Ya mahaifina ni Zainab na kubutar da Abul’asi har sau uku Nana Zainab ta maimaita wannan Magana.

Bayan Manzon ALLAH {saw} ya idar da sallah sai yace : yaku muta ne kokun ji abin da naji ? suka ce E, munji ya Manzon ALLAH.

Sai yace dasu to na rantse da Allah bansan da wannan al’amari ba sai yanzu, to amma musulmai tsintsiya daya ne karminsu yakan iya zartar da hukunci kamar yadda babba zai zartar, don haka na zartar da hukuncinki ya Zainabau

Bayan Manzon ALLAH {saw} ya shiga gida sai Nana Zainab tace da Manzon ALLAH {saw} don ALLAH baba kayi umarni adawo masa da dukiyarsa da aka kwace.

Sai manzon ALLAH {saw} yace da ita : ke dai kisani cewa bazaki iya kubutar da shiba kuma bazaki iya kwato shiba, sai taci gaba da yiwa Manzon ALLAH {saw} magiya a karshe dai manzon ALLAH {saw] ya fita daga gida ya fito inda sahabbansa suke yace dasu:

“Ku sani wannan mutun namu ne kuma yana daga cikin wada aka karbe dukiyarsa to da dai zaku kyautata da kun dawo masa da dukiyarsa na daga duk abin da aka karba a hanunsa, idan kunyi haka to nafi son haka, idan kuma kun hanashi to hakkin kune wanda Allah ya halatta muku ba kuma kune mafi cancanta da shi. Nan take sahabbai suka daga sautinsu a tare suka ce “Zamu mayar masa dashi ya Annbin Allah.

Nan take sahabbai suka dinga fito masa da kayansa sai da suka fito masa da kayansa baki daya sannan aka mika masa. Sai Abul’asi ya harhada kayansa ya nufi garin Makka.

Zuwan Abul’asi ke da wuya ya mikawa duk wani mai hakki hakinsa , duk wani wanda ya bashi sallahu sai da Abul’asi ya bashi kayansa, sai yace da muta nen Makka yanzu ko akwai wanda yake bin wani abu?

Suka ce a’a ba mai binka ya sake cewa shin kona cika alkwarin da kuka bani ? suka ce tabbas ka cika mana alkawari kuma Allah ya biyaka da alkairi.

To kusani cewa ni daga yau dinnan na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma na shaida na tabbata cewa Muhammadu bawan Allah ne kuma Manzon Allah ne.

Kuma kusani cewa babu abinda ya hana in musulunta tun a hanunsu sai don kada ku zaci ina so incinye dukiyoyin ku ne , to amma yanzu tunda Allah madaukakin sarki yasa nadawo muku da dukiyoyinku na musuluta daga yau.”

Abul’asi ya juyo ya nufi gari madina inda Manzon ALLAH {saw} yake, bayan ya mayar da hakin al’umma .

Bayan wannan sahabi ya musulunta sai Manzon ALLAH {saw} ya mayar masa da matarsa bayan ya daura musu sabon aure , harma a karshe suka haifi ya’ya biyu wato Umamatu da Aliyu.

Wannan shine bayanin yadda runduna ta Uku a musulunci ta kasance ku saurare mu a runduna ta Hudu.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

  1. […] post Runduna Ta Uku Rundunar Zaidu Dan Harisatu Ya Jagoranta. appeared first on Alummar […]

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »