Tarihin Sheik Dr. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu
An haifi Dr. Muhammad Sani umar Rijiyar Lemo a ranar 1 ga watan Juli na shekarar alib 1970, a birnin Makka na kasar Saudi Arebiya.
Dr. Muhammad Sani Rijiyar Lemo Yayi kuruciyarsa ne a unguwar ‘yan mata dake birnin Kano, Nijeriya. Dr. Lemo yayi Firamarensa a makarantar Khairul Bariyya Islamiya da kuma Primary School Kano a shekarar alib 1978 zuwa 1983.
Dr Lemo yaci gaba a makarantar sakandire (H.I.S) a Shahuci dake Kano a shekarar Alib 1987, kuma ya wuce Government Arabic Teachers College dake karamar hukumar Gwale inda a nan ya kammala Babbar sakandirensa a shekarar alib 1989.
Dr Muhammad Sani ya samu gurbin karatu a tsangayar Ilmin hadisai ta jami’ar musulunci ta Madina in da ya kammala digirinsa na farko a Kimiyyar Hadisi wato (Hadith Science and Islamic Studies) a shekarar alib 1994, da digirinsa na biyu duk dai a fanni daya a shekarar alib 2000.
Kasancewar nuna sha’awarsa ta ilmi mai zurfi da bincike, malam ya zarce da karatun digirinsa na uku a nan jami’ar musulunci ta Madina.
Dr. Sani Muhammad Rijiyar Lemo yayi karatun littafai masu yawa a wajen malamai da dama a nan gida Nijeriya da kuma Saudi Arabiya, wadanda suka hada da:
- Malam Hamza Adakawa (Akhdari, Arbauna hadisan, Ishriniya, Hamziyya da sauransu),
- Mal. Sani Inuwa (Nahwu da Sarfu),
- Mal.Mahbub Abdulkadir Sumaly (Balaga),
- Mal. Bashir Hasan (Adab),
- Mal.Aminu Mahe (Tarikh).
Haka zalika Daga cikin malamansa na saudiyya kuwa akwai irinsu:-
- Sheikh Abdulmuhsin Al-Abbad (Tauhid),
- Sheikh Ali Abdurrahman Alhuzaifi limamin Madina (Tauhid),
- Sheikh Abdulaziz Abdullatif (Jarh Wattaadil),
- Sheikh Muhammad Matar (Tadwin da Ruwat),
- Sheikh Dr. Hafiz Alhakami (Musdalahul hadis),
- Sheikh Dr.Muhammad Nur Saif (Musdalahul hadis),
- Sheikh Dr.Abdussamad Abid (Musdalahul hadis),
- Sheikh Dr. Umar Hawiyya (Tafsir)
- Sheikh Dr. Faihan Almudairi (Fiqh).
Dr. Muhammad Sani Rijiyar Lemo ya halarci tarurrukan karawa juna ilmi da kwasa-kwasai da dama a nan gida Nijeriya da kasashen Saudi Arabiya, Sudan, Mali da sauransu.
Wasu daga cikin rubuce- rubucen Dr. kuwa sun hadar da:-
- Shahr bn Haushab:Tarihinsa da maganganun malamai a kansa”(An Rubuta da larabci a Madina, a shekarar alib 1999).
- Dhawabit Al-Jarh wat Taadil inda Al hafiz Azzahabi (wanda aka buga a London a shekarar alib 1995)
- Gyara tare da Tahkikin littafin “Al Ighrab” na Imam An Nasai (An buga a Madina shekarar alib 1995)
- Gyara da Tahkikin littafin “Attamyiz fi Talkhis Ahadiis sharh al wajiz” na ImamAl-Hafiz (bugun Adhwa As salaf, Riyad Saudi Arabiya, shekarar alib 2005)
- Al-Madarasatul Hadasiyya fi Makka wal Madina”(An buga a Darul Minhaj, Riyad a shekarar alib 2005).
Dr. Muhammad Sani Rijiyar yana koyarwa a jami’ar musulunci dake Katsina a Najeriya.
Bugu da kari Dr. Muhammad Sani Rijiyar Lemo yana rike da mukaman wasu Kungiyoyi kamar su:
- Babban darakta na cibiyar bincike ta Imamul Bukhari dake Rijiyar Zaki, Kano.
- Shugaban cibiyar Sheikh Ja’afar Islamic Documentation Center (SJIDC) dake Kano.
Dr Muhammad Sani Rijiyar Lemo, yana zaune a birnin Kano da iyalinsa.