Shin Kokinsan Yadda Zaki Ajiye Ruwan Nama Da Kika Dafa?

0 748

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Shi dafafen ruwa nama Sulale ruwa ne wanda idan an dafa nama yake raguwa musanman idan naman da yawa.

Kuma nasan cewa uwargida tasani indai kinason mai gida da mutanan gida suji zakin miya to zatayi amfani da ruwan dafafen Nama (Sulale), domin yana da sundarai masu yawa da zaisa kiji miyarki Carkwai.

Kasancewar 31-07-2020 shine daya ga watan babbar sallah naga yadace mu kawo muku yadda zaku adana ruwan Namanku da kuka dafa domin ku soya, shi wannan ruwan Nama zai kaiku watani masu tsawo matukar kun adanashi yadda zamuyi muku bayani.

Yar uwa da farko bayan kin dafa namanki yakawo dai dai yadda zaki tsame ki fara soyawa, saiki samu wani abu ki ajiye dafafen ruwan Naman nan (Sulale) idan kin gama aikin soya Namanki. Saiki samu tukunyar da zata dauke adadin ruwan dafafen Naman (Sulale), saiki dora a wuta kifara dafa wannan dafafen Ruwan Naman (Sulale).

Zakiyi ta dafashi har sai kinga ruwan ya fara konewa mansa zai taso sama gaba daya kicigaba da sa wuta zakiga ruwan ya kone harma man yadan fara soyuwa bata konewa ba saiki sauke.

Zaki samu ruba mai murfi misalin irinta fenti saiki zubashi a ciki ki rufe sosai yadda iska bazata dinga shiga ba, saiki ajiye kayanki duk lokacin da zakiyi amfani dashi saiki samu cokali mai kyau wankake saiki dinga deba kina amfani dashi idan bukatar hakan ta tashi.

Yaruwa wannan abu dakikai zai iya kaiki har wata 7 zuwa 8 bai lallace ba, Allah ya temak a kumayi sallah lafiya.

Ina fata zakiyi sharing zuwa WhatsApp ko Facebook don yan uwa mata su amfana .

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »