Takaitaccen Tarihin Abubakar Imam

0 1,283

Abubakar Imam O.B.E C.O.N L.L.D (Hon.) N.N.M.C. marubuci ne, ɗan jarida kuma ɗan siyasa, A tsawon rayuwarsa, ya zauna a Zariya, inda ya kasance editan Hausa na farko na Jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo, Jaridar Hausa ta farko a Arewacin Najeriya.

An haifi Abubakar Imam a Kagara dake jihar Neja a Najeriya, a ranar 1 ga watan Fabrairu na shekarar alif 1911, ya rasu a shekarar alif 1981 a ƙalla yana da shekaru 69 zuwa 70.

Ya halarci Kwalejin Katsina da kuma Cibiyar Ilimi ta Jami’ar Landan. Ya fara shahara ne a lokacin da ya gabatar da wasan kwaikwayo na Ruwan Bagaja a gasar adabi a shekarar alif 1933. Alkalin gasar shi ne Rupert East, shugaban kwamitin fassara. Ya ji daɗin rubuce-rubucen nasa, saboda sanin ƙayyadaddun ƙa’idodi da suka ba sha’awa kuma ya gauraye da salon wallafe-wallafensa na hikima da ƙagaggun labari.

A shekarar alif 1939, shi da Robert East da wasu mutane, suka kafa kamfanin buga jaridu na Gaskiya corporation, wanda ya samu nasara kuma ya samar da dandali ga ɗimbin masana a Arewacin Najeriya.

Fitowar manyan marubuta da dama a Arewacin Najeriya kan harkar siyasa ya sa Imam ya shiga siyasa. A shekarar 1952, da aka kafa jam’iyyar NPC ta Arewa, tare da Umaru Agaie da Nuhu Bamalli, suka kafa babbar cibiyar gudanarwa na jam’iyyar.

Alh Abubakar Imam ya shine mawallafin littafin Magana Jari Ce tare, littafin Ruwan Bagaja da Tafiya mabudin ilmi, littafi ne da ya rubuta kan abubuwan da ya faru bayan ya ziyarci Landan.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »