Tuffa ‘yar itaciya ce mai kyan gani ga kuma dadin ci, wanda mafiya yawan mutane Kanci Tuffa ne kawai don daɗin ta Basu san muhimmancin ta ga lafiyar jikin su ba.
A wannan rubutu zamu bayyana muku muhimmancin cin Tuffa ga lafiyar jikin dan Adam. Kamar haka:
Kyautata Lafiyar Hakora da saka su Haske.
Tauna Tuffa yana rage kwayoyin cuta dake kama hakora yana kuma maganin ruɓewar hakora tare da saka su haske.
Saukaka Tauna Abinci.
Tuffa tana samar da miyau a cikin baki. Wanda ke taimakawa wajen tauna abinci da hadiyarsa cikin sauqi tare da hana bushewar maqogwaro.
Rigakafin Cutar Kansa (cancer).
Cin Tuffa yana da kashi 23 bisa 100 na rage hadarin kamuwa da cutar kansa.
Rage Hadarin Kamuwa da Cutar Deabetes.
Matan da suke cin Tuffa aƙalla guda daya a rana, suna da kariya 28 bisa 100 sama da wadanda basa ci, daga kamuwa da cutar deabetes type 2.
Rage Kitse/ƙiba.
Tuffa tana da sinadaran da ke rage kitse/ƙiba daga cikin hanjin mutum tare da samar masa da ingantacciyar lafiya.
Lafiyar Zuciya.
A cikin Fatar Tuffa, da akwai sinadaran da ke daidaita shige da ficen jini a cikin zuciya tare da ba ta ingantacciyar lafiya.
Maganin Ciwon Kai.
A feraye Tuffa a ci banda 6awon yana taimakawa sosai wajen maganin ciwon kai.
Cushewar Ciki.
Shan Tuffa hade da Zuma yana maganin cushewar ciki da ke hana cin abinci.