Domin Wanke Fuska Tayi Kyau

0 845

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

A samo wadan nan abubuwan kamar haka:

1- Zuma babban cokali 2,

2- Karamin cokali na garin ‘ya’yan Almond ( da turanci) Lauz (da larabci).

3- Karamin cokali na lemon tsami.

Sai a kwaba su a rika gogawa a fuskar, sannan sai a wanke da ruwan dumi. Insha Allahu za a ga sauyi sosai cikin hikimar Allah.

KARIN BAYANI.......

Na san ba kowa ne yasan Lauz ko Almond ba, wata itaciya ce mai yin ‘ya’ya kamar na dabino tana fitowa ne a kasashen larabawa da gabas ta tsakiya. Ana samun ‘ya’yanta da Manta a kasuwanin da ake siyar da kayan maganin Islamic.

Har yanzu fa wasu basu gama gane menene ALMOND ko LAUZ din nan bafa…..

Amma na san dai kunsan bishiyar Umbrella ko? Ai itace Almond kuma lauz din.

To yayanta sai a fasa kwallon akwai wata yar gyada a cikin kwallon, to shi ne ake amfami da shi.

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »