KARIN GASHI YAYI TSAYI SANNAN KUMA YAYI YAWA GAMI DA BAKI.
ABIN BUKATA
- Kwai Danye.
- Roba mai Kyau mai dan fadi
YADA ZAKIYI
Kisamu wannan kwan naki saiki dauko wannan roba taki saki fasa wannan kwan saiki cire kwaiduwar kwan ma’an wannan yallon abin na ciki ki ajiye gefe daya.
Saiki juye farin ruwan kwan a wannan roba taki.
Idan gashin naki da dan yawa saiki fasa kwan kamar uku-kodai yada yasamu.
Saiki dinga diban wannan farin ruwan kwan kina shafeshi a gashin naki, har saikin tabbatar cewa
ruwan kwan ya ratsa ko ina cikin gashin naki.
Saiki barshi tsawon mintuna 20 ko 30 saikiwanke kan naki da sabulu mai kyau kina iya amfani da sabulun Allo berra.
Kada kimanta cewa gashi yakan sanya mazaje kara kaunar matayensu.
ALLAH ya temaka.