DAN MASANIN KANO YUSUF MAITAMA SULE
An haifi Yusuf Maitama Sule a Shekarar alib 1929, a unguwar Yola, cikin garin Kano. Maitama shi ne na uku a jerin ‘ya’ya a gidansu, sauran yan’uwa biyu mata ne; wato, Rabi, wacce ake kira Yaya ta Zagi, Maimuna wacce ake kira Yaya ta Bichi.
An sa masa suna Yusuf, saboda sunan Mahaifin Madakin Kano Mahmudu, shi Madaki yana kiran shi Abbana. Sunan Maitama kuwa an sa masa shi ne saboda Galadiman Kano Yusuf, saboda an yi amfani da makamai sosai lokacin basasar Kano. Akan yi wa duk wani mai suna Yusuf lakabin Maitama.
Marigayin shahararren dan siyasa ne a Najeriya, wanda ya taba rike mukamin minista da kuma jakadan kasar a Majalisar Dinkin Duniya.
Ya zama minista lokacin Firai Ministan Najeriya na farko Alhaji Abubakar Tafawa Balewa.
Hakazalika, galibin mutane za su rika tuna wa da marigayin ta wajen yadda ya kware wajen iya magana.
A shekarar 1976 ne aka ba shi kwamishinan gwamnatin tarayya mai kula da korafe-korafen jama’a.
Yayin da a shekarar 1979 ya tsaya takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar NPN, sai dai Shehu Shagari ne ya lashe zaben.
Har ila yau, gwamnatin Shagari ta nada shi jakadan Najeriya na dindindin a Majalisar Dinkin Duniya watanni bayan kammala zaben.
A can ne ya jagoranci Kwamitin Musamman kan Yaki da Wariyar Launin Fata na majalisar, wanda masu sharhi ke ganin ba karamin matsayi ba ne.
Hakazalika, bayan da Shugaba Shagari ya lashe zabe a shekarar 1983 ya sake nada shi Minista Mai Kula da Tafiyar da Kasa, wato mai taimakawa shuagabn kasa kan yaki da cin hanci.
An taba ruwaito shi yana cewa: “Kowane mutum yana da baiwar da Allah Ya yi masa. Allah Ya ba ‘yan arewa kwarewa ne wajen shugabanci. Bayarabe wajen dogaro da kai da kuma kyawawan dabi’u. Igbo suna da baiwa wajen kasuwanci da kuma kere-kere. Allah Ya halicce mu daidai kuma kowa da baiwar da Ya yi masa.”
Wasu sun yi amfani da wannan kalami nasa wajen bayyana damuwa game da yadda ‘yan arewa suka mamaye fagen shugabancin kasar.
A shekarar 1957 gabanin Najeriya ta samu ‘yancin kanta, marigayi Maitama Sule shi ne ya kewaya da Sarauniyar Ingila Elizabeth yayin da ta kai ziyara Kano yana yi wa jama’a bayaninta.
Kafin rasuwarsa a ranar Litinin, Dan masanin Kano, Alhaji Yusuf Maitama Sule, ya taka rawa sosai a fannoni daban-daban a Najeriya, inda ya zamo daya daga cikin mutanen da suka fi fice da kuma kima a kasar.
Yarasu Ranar 3 ga watan Yuli 2017 Akasar Masar, Ya rasu ya bar ‘ya’ya 10 Maza hudu, Mata shida.
Allah Yajikansa Da Rahma Ameen