YADDA ZAKIYI DAKUWA

0 1,331

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

KAYAN DA ZA KI TANADA

  1. Aya
  2. Jar dawa
  3. Masoro
  4. Citta
  5. Barkono
  6. Kanunfari
  7. Sikari
  8. Kuli-kuli ko gyada
  9. Man gyada

YADDA ZA KI HADA


Dakuwa tana daya daga cikin kayan gara da ake kai wa amare a kauye, ko kuma idan an yi haihuwa. A birni ma ana kaiwa lokacin da ake yiwa amarya gara, amma a zamanin dane wannan yanzu an daina.

Sai dai kawai ka ga ana yin ta domin sayarwa. Manya da yara duk suna cin dakuwa.

Yadda ake yin dakuwa kala biyu ne, da wadda ake yi da jar dawa (kaura) da kuma wadda ake yi da aya. Za mu kawo muku yadda ake yin duka biyun.

DAKUWAR DA AKE YI DA AYA


Ki sami aya ki wanke ki rege idan da akwai tsakuwa kenan, sannan ki shanya ta ta bushe, sai ki soya ta, idan tayi sai ki kai inji a barza. Idan an dawo da ita sai ki zuba a turmi kifara dakawa, ki kawo gyada ko kuli-kuli ki zuba, amma gyadar ba a soya ta da gishiri, ki zuba kayan kanshi wato barkono da citta da masoro da dan gishiri dan kadan kicigaba da dakawa.

Haka za ki yi ta dakawa har sai kin ga ta fara dunkulewa tana curewa, idan kina so ma kina iya zuba dan man gyada ko na kuli dan kadan domin ta cure sosai ta hade.

Idan kin ga ta cure sosai tana dunkulewa kuma tana kyalli tana naso to ta daku kenan sai ki kwashe ta daga cikin turmi ki cuccura yadda ki ke so.

DAKUWAR DA AKE YI DA JAR DAWA

Ki sami jar dawarki da ake kira kaura ki wanke ki rege ki shanya ta ta bushe, idan ta bushe sai ki soya ta.

Sai ki kai inji a nika miki, idan an dawo da ita daga nika sai ki sami rariya mai laushi ki tankade, mai laushin sai ki zuba a turmi, ki kawo kuli-kuli ko gyada ki zuba da sikari da masoro da cittadan barkono ki zuba ki yi ta daka.

Haka zaki cigaba da daka har sai kin ga ta daku sosai komai da kika zuba a ciki ya hadu ya cure waje daya. Idan kina so ta kare hadewa da curewa waje daya sai ki dan zuba mai kadan ki daka.

Idan tayi sai ki ciro ki cura son ranki.

Masha Allah aci dadi lafiya kuma a TURAWA JAMA’A.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »