Dangane da su wa suka kafa jam’iyyar kuwa, kamar yadda aka bayyana a baya ƙungiyar wasu mutane ne da ake kira G-34 tare da wasu ƙananan ƙungiyoyi kusan guda 125 ne suka haɗu suka kuma amince da kafa jam’iyyar PDP (Odunayo, 2016). Kodayake, yawanci an fi danganta kafuwar jam’iyyar ga membobin ƙungiyar G-34, ba don komai ba sai kasancewarsu kanwa uwar gami dangane da fafutukar neman komawa ga mulkin dimokuraɗiyya.
Waɗanda aka tabbatar su ne mambobin G-34, waɗanda kuma ake alaƙanta kafuwar jam’iyyar PDP zuwa gare su, su ne:
- Abubakar ɗanMusa
- Abubakar Olusola Saraki
- Abubakar Rimi
- Adamu Ciroma
- Ahmadu Ali
- Alex Ekwueme
- Aminu Wali
- Ango Abdullahi
- Atiku Abubakar
- Audu Ogbe
- Bamanga Tukur
- Barnabas Gemede
- Bello Kirfi
- Bola Ige
- Daniel Saro
. - Garba Nadama
- Isiyaku Ibrahim
- Iya Abubakar
- Iyochia Ayu
- Jerry Gana
. - Jibril Aminu
- Jim Nwobodo
- Lawal Kaita
- Musa Musawa
- Sani Zangon Daura
- Solomon Lar
- Sulaiman Kumo
- Sule Lamido
- Sunday Awoniyi
- Tanko Yakasai
. - Tom Ikimi
- Tony Aneni
- Walid Jibril
- Yahaya Kwande.
Marubuci:
Jibril Yusuf
Usman Danfodiyo University Sokoto