SASSAƘE
Sassaƙe na nufin yin amfani da fatanya ko magirbi ko dai wani abin wajen ciro ɓawo daga jikin wata bishiya domin a sarrafa ta a yi magani misalan kaɗan daga cikinsu sun haɗa da:
- SASSAKEN MARKE
Ana sassaƙo bishiyar marke a dafa idan ya huce sai a ɗiba a haɗa da lemon tsami a rinƙa sha yana maganin tari.
- SASSAKEN ARARRABI
Ana jiƙa sassaƙen Ararraɓi a rinƙa sha yana maganin tau-tau, bayan haka ana shanyawa ya bushe a daka a rinƙa barbaɗawa a kan tau-tau ɗin.
- SASSAKEN KIRYA
Ana Amfani da sassaƙen ƙirya ana jiƙa shi da ruwa a sha yana maganin ciwon jiki.
- SASSAKEN TAURA
Ana amfani da sassaƙen taura a jiƙa a sha yana maganin (Tamama) jin-kashi wanda yara ke fama da shi.
- SASSAKEN MARKE
Ana jiƙa sassaƙen marke a ruwa a ba mata masu ciki wata huɗu idan yana yi musu ciwo domin samun lafiyar cikinsu da jaririn da suke ɗauke da shi. Bayana haka ana shanya sassaƙen marke ya bushe a daka a haɗa da irin gero idan za a shuka domin samun kyakkyawan sakamako, sannan kuma baya burtuntuna, har ila yau ana haɗa sassaƙen marked a jar-kanwa a sha maganin tari.
- SASSAKEN SHIRINYA
Ana jiƙa sassaƙen shirinya da ruwa a rinƙa ba yara suna sha maganin mafarkin yara. Kinkiba.
- SASSAKEN TUMFAFIYA
Ana kankare sassaƙen tumfafiya a haɗa da nono a sha maganin shawara.
- SASSAKEN BAKIN MAKARHO
Ana sassaƙar baƙin-maƙarho a jiƙa da ruwa har tsawon kwana uku, a rinƙa sha maganin basir mai tsiro.
- SASSAƘEN FARAR ƊORAWA DA SASSAƘEN MANGWARO
Ana amfani da sassaƙen farar ɗorawa da sassaƙen mangwaron a jiƙa da jar-kanwa a sha maganin basir.
- SASSAKEN KWANARYA
Ana dafawa da nonon saniya a riƙa sha yana maganin shawara, bayan an sha ana yin amai, ana warkewa sarai.
- SASSAKEN GAWO
Ana jiƙa sassaƙen gawo da ruwa a sha yana maganin taurin kai, musamman ‘yan tauri ko ‘yan daba.
- SASSAƘEN GOBA DA MANGWARO DA LEMON TSAMI:
Ana amfani da su wajen maganin ciki, ana shanya su, su bushe sannan a daka a rinƙa jiƙawa ana sha yana maganin ciwon ciki.
Great post