Shin Ko Kinsan Bayyana Kwaliya Kan Gayyato Shedanin Aljani Su Shiga Jikinki

0 184

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

BAYYANA KWALLIYARKI GA KOWA YANA GAYYATO SHEDANIN AlJANI SHIGA JIKINKI

“Bayyana kyau da kwalliyar mace ko namiji da yadda suke barin jikinsu ko tsiraicinsu a waje, suna iya sabbaba Shedanun Aljanu shiga jikinsu surika soyayya da su har su rika sanya musu kyamar yin aure ko kuwa rusa duk wani dalilin da zai sa su suyi auren.

Sai kaga mata da yawa ciki har da matan Aure suna ta daukar hoto suna yadawa duniya ba tare da Hijab ko niqab ba, yoo ko ma da Hijab da niqab dinne wa yace miki ki rika yada hotunanki a social media? Allah ya bayyana iya adadin wadanda za ki iya nunawa kwalliyarki matar Aure ce ke ko mara aure.

Idan kin tura hotonki a social media shin kina tunanin iya masoyankine kadai za su gani banda makiyanki da mahassadanki? Kina tunanin iya mutanene kadai za su gani banda Aljanu? Kina tunanin masu Kambun-baka da Kambun-Ido da masihirta da matsafa bazsu iya ganin hoton ba? Kuma wadan nan duk abu ne mai sauki su iya cutar da ke ta wannan fannin.

Kibar ganin ai hoto ne kawai, wallahy yar uwa lamarin ya fi gaban haka. Kawai idan har kuna son zaman Lafiya a rayuwarku to abi dokar Allah sai a zauna lafiya.

Kuma hakan ma na iya faruwa ta fannin sihiri inda za a tura shedanin Aljani yarika wannan aikin a jikin mace ko namiji na hana su Aure abisa umarnin da Boka yabashi.

Kuma Hassada da Kambun-baka ma Jinnul Aashiq na iya maqalewa da su ya rika irin wannan aikin a jikin mutane.

Amma duk waɗannan suna faruwa ne da sanin Allah da kuma yardarSA, saboda babu abinda yake faruwa a bayan sanin Allah.

MAFITA:

A rika rufe jiki gaba daya musamman ma ga mata, adaina fitar da tsiraici da kallon tsiraicin wasunku, ki daina yada hotunanki a duniya, a daina sabawa Allah a fili da boye saboda ananne shedanun Aljanu ke ganinku sai suyi sha’awarku a karshe kuma su shige jikinku, su hana ku Aure ko zaman lafiya a gidajen auren ku.

Matukar mutum yana yawaita karatu da sauraron Alqur’ani, yana Azkaar musamman na shiga toilet da fitowa, sanya tufafi da cirewa, shiga gida da fita, cin abinci da gamawa, na safe da maraice, kwanciya bacci da tashi, to in Sha ALLAHu zai samu kariyar Allah daga dukkanin sharrin halittunSA.

Amma idan mutum yayi watsi da Azkaar sai kaga Allah ya sanya Shedan ya zama abokinsa kullum suna tare, yayita wahalar da shi ya hana shi zaman lafiya kuma yasanya shi kullum yana wajan bokaye da yan bori, saboda ya mantar da shi ALLAH sai shima ALLAH yamanta da shi kansa yakasa aikata abinda zai amfaneshi a duniyar shi da lahirarshi yayita wahala, a ƙarshe kuma Allah yasanya shi a Wuta matukar bai tuba ba kafin mutuwarsa.

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)

Domin karin bayani:
👇👇👇

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »