Wasu Alamomin Kambun Baka Ga Yara.

0 474

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

ALAMUN TASIRIN KAMBUN-BAKA GA YARA

1- Yawaita yin kuka cikin dare akai-akai ba tare da wani dalili ba.

2- Aji jikin yaro yarika yin zafi.

3- Rashin nauyin jiki.

4- Rashin yin bacci .

5- Launin fuskar yaro yarika sauyawa.

6- Rashin Annashuwa, kullum yaro cikin damuwa abu kadan sai ya fusata.

7- Yaro yazama ba ya jin magana ( Kamar a hana shi aikata abu amma yaki hanuwa).

8-Karkacewar kwayar idon yaro zuwa bangaren hagu ko dama.

MAFITA:

Da zarar an fahimci yaro yana fama da wannan matsalar sai a samo ruwa mai tsarki da tsafta kamar wanda zai cika karamin botiki, sai a sanya ganyen magarya kamar guda 7 ko 9 bayan an dandange shi, ko ganyen Garafuni, ko Tazargade duk wacce aka samu cikinsu ya yi ko a zuba su su duka a cikin ruwan.

Bayan haka sai a karanta wadannan Surorin da Addu’o’in a cikin ruwan:

1- Suratul Fatiha ( Sau adadin da za aka iya)

2-Ayatul Kursiyyu (Sau adadin da za ka iya)

3- Ikhlas ( Sau adadin da za ka iya).

4-Fakaqi (Sau adadin da za ka iya).

5- Nasi (Sau adadin da za ka iya).

6-
أعوذ بكلمات الله التامات من غضبه وعقابه ومن شر عباده ومن همزات الشياطين وأن يحضرون.

“A’UZU BIKALIMAATILLAHI ATTAAMMAT MIN GADHBIHI WA IQAABIHI WA MIN SHARRI IBADIHI WA MIN HAMAZAATISH SHAYAATYN WA AN YAHDURUN.”(Sau adadin da za ka iya).

7-
أعوذ بكلمات الله التامة من كل شيطان وهامة ومن كل عين لامة

“A’UZU BIKALIMATILLAHI ATTAAMMAH MIN KULLI SHAITAANIN WA HAAMMAH WA MIN KULLI AININ LAAMMAH.” (Sau adadin da zaka iya).

8-
أعوذ بكلمات الله التامات من شر ما خلق.

‘A’UZU BIKALIMATILLAHI ATTAAMMAAT MIN SHARRI MAA KHALAQA.” (Sau adadin da zaka iya).

Sai arika masa wanka ana ba shi yana sha (Idan yana shan nono itama uwar sai ta rika sha) kullum safe da rana da dare.

Kuma a karantasu a cikin zuma sai a rika lasa masa a baki a koda yaushe, ko ya rika shan karamin cokali.

Kuma a tofa su a cikin man zaitun ana shafa masa a duk jikinsa safe da dare, in sha ALLAH za a dace. Allah zai kawo waraka.

Mujarrabi ne wannan ba sau daya ba ba sau biyu ba. Amma komai sai da izinin Allah.

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »