An Koya Min Darasi {02} Labarin Wata Budurawa.

0 282

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

AN KOYA MIN DARASI {02}

Tace….

Budurwa ce ni, an kawo min kudin aure har an sa min rana, har yarage sati biyu masu zuwa ne Aure na. Ina son shi matuka kuma shi ma haka, mun fahimci juna sosai fiye da yadda kowa ke zato.

Sai kwatsam wata rana wata makobciyar mu ita bazawara ce, sai tace : Wance!

Na amsa nace : Na’am,

Sai tace: Anya kuwa ba zakije a duba muku taurarinki ke da wanda za ki aura ba saboda tsaro?

Nace: Ai to Aunty wance, tunda dai mun fahimci juna da shi ai ina ganin babu wata bukatar dube-dube a cikin lamarin nan Addu’a kadai muke bukata.

Nan dai matar ta matsa sai da na amince gidanmu ma ba’a sani ba, ta sa ni a gaba sai da mukaje gidan wani malami sai kuwa malamin ya nuna Lallaikam taurarin mu sun nuna auren mu akwai matsala ba karama ba kuwa.

Na tsorata sosai, sai kawai shedan yayi galaba akaina, nan take tuni auren ya fita raina, nazo gida na nuna musu nifa kawai su fasa auren nan su mayar masa da kudinsa, sukayi sukayi na fada musu dalilina amma naki fadi…

Yanzu ga shinan an doshi wajan Shekaru 5 da wannan lamari, shi har ya yi aurensa da yara 2, Ni kuma ga ni nan ina ta gararanba a gari babu tsayayye sai tarin yan iskan samari kamar wata tsohuwar bariki. 😭

Ina kira ga mutane masu irin wanna halin da na shiga ciki na son zuwa wajan Malamai a duba musu kaza da kaza, su daina su dogara ga Allah kawai ya wadatar da su. Su saba da yin Sallar Istikhara Wallahy inba haka ba kuwa za ku shiga halin da na shiga ko ma wanda yafi nawa.

Allah ya kyauta….

Gani ga wane….

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »