Amfanin Bawan Kwakwa Wajen Kashe Guba

0 735

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Idan mutum yasha guba (poison) a rashin sani sai ayi gaggawar hada masa wannan hadin na bawon kwakwa 🥥, yadda ake hada shi shi ne kamar haka:

Za a samo bawon kwakwar ne sai a kona shi a cikin wuta har yayi baki kamar yadda yake a cikin hoton can, sai a daka shi ayi garin shi yayi laushi sosai sai a rika dibar garin cokali 3 ana zubawa a ruwan dumi kimanin kofi daya kafin a sha a tabbatar an kada shi kuma an gauraya shi da kyau.

Sai a baiwa wanda yasha guba (Poison) din yashanye, IN SHA ALLAHU za kuga ya amayar da gubar da yasha da YARDAR ALLAH.

Kamata yayi a samu garin bawon kwakwar a ajiye shi sbd gudun ko-ta-kwana ko kuma taimakon gaugawa.

Amma kuma a rika lura da abinda ake ci ko ake sha saboda tsaro kuma duk halin da kake ciki kar ka ksukura ka ki ambatar BISMILLAH kafin kaci ko kasha wani abu.

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »