Muhimmancin Ɗanyar Kubewa Ga Mata.

0 1,347

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Kubewa tana karawa mata ni’ima, ko da ace kuwa mace ta bushe to idan har ta dage da amfani da ita tana samun mafita ta ban mamaki da yardar Allah.

Kubewa tana daga cikin abincin da yake karo ovulation (kwayayen halitta) din mace ga wacce take da matsalar kwayayen halitta, har ma ya lullunka kwayayen wato ( Hyper ovulation) tayadda za suyi yawa sosai, kuma hakan ka iya sanyawa cikin ikon Allah a iya samun haihuwar yan biyu ( Twins) kamar yadda masana kimiyya suka fadi.

Kubewa tana dauke da sinadaran ZINC, FOLATES, IRON da kuma VITAMIN-B wadanda duk suna da amfani ga bincika da kuma jin dadin mu’amilar saduwar aure.

YADDA AKE AMFANI DA ITA

1- Za a iyayin miyar danyar kubewa amma yadda baza a barta ta dahu sosai ba har yaukinta ya ragu ko yagushe ba, anaso ne a cita ko a shata da yaukinta sosai.

Shima ganyenta ana iyayin miya da shi kamar yadda binciken yatabbatar shima yana da amfani sosai kamar yadda Kubewar take da shi. Allahu A’alam.

2- Ko kuma a samu kamar kwayar kubewa 5 sai a yayyanka kubewar sala-sala sai a sanya ta a cikin roba/gora a zuba ruwan sanyi a ciki da dare sai ya kwana a jike, a cire kubewar a cikin ruwan sai a shanye ruwan da safe.

Mace mai bukatar kwayayen halitta za tayi amfani da kubewar ne bayan ta yi tsarki daga Al’adarta za ta dau kwanaki 2 zuwa 3 tana amfani da Kubewar.

Mai matsalar ni’ima kuma ko dandanon saduwar aure to za ta rika shan miyar Kubewar ne akai akai, wasu ma idan auren diyarsu ya kusa kamar sati daya sai duk satin ba miyar da za ta rika sha sai miyar Kubewa.

ABIN LURA

Ba wai na ce kubewa tana sanya haihuwa bane, ko tana sanyawa a haifi Twins ba a’a. Allah ne mai bayar da haihuwa ga wanda yaga dama kuma shike bayar da kyautar yan biyu ga wanda yaga dama, amma akwai sabubba na ilimi wanda likitoci ke bayaninsu ko a al’adance amma duk wannan sabubban ba zasu taba iya tabbatar da abinda Allah bai tabbatar ba.

Tabbas kubewa tana da amfani wajan boosting din kwayayen halitta, tana magance matsalar Infertility, tana karawa mata ni’ima da yardar Allah. WALLAHU TA’ALA A’ALAM.

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)

Domin karin bayani:

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »