Takaitaccen Tarihin Maryam Shatty

0 350

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

An haifi Maryam Shettima da aka fi sani da (Maryam Shatty) a jihar Kano, a ranar 8 ga watan Afrilu Shekarar alif 1979. Ta kamala karatun ta na Firamare da Sakandare dukka a Jihar Kano.

Shatty Ta yi Digirinta na farko a Jami’ar Bayero da ke Kano, inda ta yi karatun ta a fannin lafiyar Ƙashi (Physiotherapy), inda ta ƙware a fannin. Ta kuma samu digirinta na biyu a Jami’ar Gabashin Birtaniya, Stratford inda ta karan ci fannin kula da ƙashi na ɓangaren wasanni.

Ta bada gudunmawa sosai a fannin likitancin ƙashi tare da kasancewarta ‘yar kasuwa, baya ga fitacciyar rawar da take takawa a fannin tallafawa mata da fadada mu’amalar ta ga shiga cikin al’umma, wanda ya sanya ta zama daya daga cikin manyan matasa masu fada a ji a cikin al’umma Afirka.

Tafara aiki tare da Dala Orthopedic da Asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano da ke Kano kafin daga bisani ta tafi Landan don ci gaba da karatunta. Ta samu Digiri na biyu a Jami’ar Gabashin Landan, Stratford inda ta karanci fannin ilimin motsa jiki.

Maryam Shatty

Shatty ta kasance ɗaya daga cikin likitocin tawagar Najeriya a gasar guje-guje da tsalle-tsalle ta Duniya da aka gudanar a birnin Landon a shekara ta 2012.

Maryam Shatty ta yi kwasa kwasai da dama a wasu cibiyoyi na ƙasashen duniya, ciki har da Amurka.

Ta samu lambar yabo ta girmamawa a Jami’ar fasaha ta ESGT ta Jamhuriyar Benin saboda rawar da ta taka a fagen jagoranci da ci gaban al’umma.

Duk da cewa ba ta taɓa yin takara ba, ta kasance ƴar siyasa a Jam’iyyar APC mai mulki. Ta kasance a cikin kwamitin yaƙin neman zaɓe na shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu.

A ranar 2 ga watan Agusta, 2023, sunan Maryam Shetty ya shiga cikin jerin sunayen ministocin da Shugaba Bola Tinubu ya zaɓa. Sai dai kash a ranar 3 ga watan Agusta, 2023, Shugaba Bola Tinubu ya cireta daga cikin Jerin sunayen Ministocin da za’a tantance. Ya kuma canza ta da Dr. Mariya Mahmoud. Wanda hakan bayyiwa Al’ummar Jahar Kano daɗi ba.

Sai dai awani Bidiyo da Freedom Rediyo a Kano Ta fitar an nuna Tsohon Gwamnan Jihar Kano Ganduje yana cewa su basu santa a siyasa, hakan yasa wasu ke zargin shine ya sanya aka cire sunan Dr. Maryam Shatty.

Maryam Shatty na da Aure har da Yara, kuma tana ɗaya daga cikin shahararrun Mata a Shafukan sada zumunta.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »