Yadda Za’a Kawar Da Kaba (Hernia)

0 59

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Duk wanda Kaba ta takura masa kuma yana son rabuwa da ita, to ga mafita nan da yardar ALLAH, Zai samo bishiyar Banana/Plantain wacce aka yanketa. Ma’ana asalin jikin bishiyar muke nifi a nan.

Sai ka bare ko ka cire duk bawon dake a gefe-gefen sai ka ciro wannan na tsakiyar mai kama da sanda, sai ka yayyanka shi guntu guntu ( iya girman dunkulen hannunka) kamar yanka 1, Sai ka shanya shi a cikin daki ba a cikin rana ba tsawon kwanaki 4, za kaga ya fara sauya kala ya koma baki ko brown haka.

Sai ka sanya shi a cikin tukunya a tafasa shi da ruwa wadatacce na tsawon mintuna 20, sai a sauke shi a rika shanshi da dumi sau biyu kullum idan ya kare sai a sake hada wani har tsawon watanni 2, sai a dakata haka ake a ga likita za kuga abin mamaki da YARDAR ALLAH.

Kuma bayan magance matsalar QABA da yakeyi yana magance wasu matsalolin dabam ciki har da bangaren mafitsara in Sha ALLAH…

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »