Muhimmun Abin Da Ya Kamata Mu Sani Lokacin Shan Shayi

0 458

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Idan har za ka sha shayi na GANYEN SHAYI (ba na Milo ko Nascafe ba) to karka kuskura ka rika sanya MADARA a cikinsa, saboda yin hakan zai matuƙar kawo wa lafiyar ka matsaloli

Saboda shi GANYEN SHAYI (a karan kansa) yana dauke ne da sinadarin “Nitric oxide”.

Ita kuma MADARA tana dauke ne da “caseinate ko Casein proteins”

Tayadda haduwar wadan nan sinadaran a jikin mutum yana iya kawo matsala ga masu fama da ciwon Qoda da kuma ciwon Hanta Hepatitis.

Amma idan za ka sha SHAYIN ne da MILO, NESCAFE ko makamantansu wannan ba matsala idan ka sanya MADARA ciki in sha ALLAH, amma zuba madara acikin ganyen SHAYI kamar LIPTON, TOP TEA, GREEN TEA, Na’a Na’a da sauransu shine matsalar.

Shan ganyen shayi shi kadai ba tare da sanya madara ba wannan shi ne yafi zama daidai game da lafiyar mu da yardar Allah.

ALLAH yasa mu kiyaye kuma mu lura…

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »