Amfanin Ganyen Lansir Ga Masu Ciwon Mara

0 491

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Mai fama da Infection din mara ko ciwon mara ko matsalar mafitsara to tayi ko yayi amfani da wannan ganyen na LANSIR.

A samu ganyen lansir kamar da dan yawa, sai a sanya masa ruwa kimanin litre 4 da citta daidai gwargwado da jar kanwa yar kadan, sai a tafasa kuma a tace a shanye duk litre 4 a yini daya, ya danganta da yadda za ka shanye litre 4 a yinin.

Za ka iya da safe kasha litre 1, Azahar kasha litre 1, la’asar kasha litre 1 sai da dare ma kasha litre 1, ko ma dai duk yadda kaga za ka iya, bukata dai shi ne ka shanye litre 4 din a yini daya. Kuma ku dau tsawon kwana 4 kuna shan maganin in Sha ALLAH za ku samu lafiya da yardar Allah.

Ana samun ganyen Lansir ne a wuraren da ake siyar da kayan lambu.

Amfanin Lansir

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)

Domin karin bayani:
👇👇👇

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »