Warin baki wani irin abu ne da yake damun mutane musamman ma shi kanshi mai fama da lalurar, har ya rika jin kunya ko kin shiga cikin mutane saboda matsalar, duk yadda yakai da tsaftatace bakinsa ko da kuwa yana yin brush sau ba adadi a rana amma za kaga warin bakin nan yana nan baya tafiya.
To dan uwa matsalar nan ba a bakinka take ba tana daga cikin cikinka ne musamman ma hanjin cikin ka, ga wata mafita nan da yardar ALLAH za ka rabu da wannan matsalar.
Ka samu abubuwan nan kamar haka:
1- Na’a na’a danye.
2- Kurkum.
3-Lemon tsami.
4- Cardamom
A tsaftace ganyen na’a na’a kuma a wanke shi da kyau, a dauko lemon tsami guda daya a wanke shi a yayyanka shi sala-sala sai a sanya garin kurkum rabin babban cokali a ciki da garin Cardamom shi ma rabin babban cokali, sai a markade su a blender sai a tace a zuba ruwan a cikin mazubin kwalba ko roba, za ka iya sanya shi cikin abin sanyayawa don yayi sanyi idna ka so hakan.
Sai ka rika shan kofi daya da safe da dare. In Sha ALLAHu za ka samu waraka daga matsalar warin da bakinka yakeyi da yardar Allah.
Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.
Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.
(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)
Domin Ƙarin Bayani Game Da Darrusan Marubucin.
+2348031542026
https://t.me/Rismawymedicine
rismawy86@gmail.com