Amfanin Ganyen Baure Ga Lafiyar Jikin Dan Adam

0 1,077

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Ka samo ganyen BAURE sai ka tafasa shi sannan ka tace shi ka rika shan kofi 1 a sanya zuma ko a sha shi haka ba komai a kullum safe da yamma, yin hakan yana da matukar amfani ga lafiyar mu kamar haka:

1- Yana karawa zuciya lafiya kuma yana daidaita jini ta yadda Allah zai kubutar da kai daga ciwon hawan jini da ciwon Diabetic da izinin Allah.

2- Yana ragewa mutum nauyin jiki, kuma ya dakatar da sinadaran da suke karawa mutum qiba, da izinin Allah.

3- Yana taimakawa wajan narkar da abinci ga wanda yake fama da matsalar rashin narkewar abinci a cikin cikinsa, da izinin Allah.

4- Yana taimakawa maza wajan sanya iyalansu farin ciki a yanayinsu na ma’aurata, da Izinin Allah.

5- Yana karawa kasusuwan mutum karfi da kwari, da izinin Allah.

6- Yana karawa idanuwa lafiya musamman ma matsalar yanar ido ga wadanda suka manyanta har ma ga wasun su, da Izinin Allah.

7- Yana bayar da kariya daga kamuwa da cutar Daji (Cancer), kuma yana karawa fata lafiya, da izinin Allah.

Wannan kadan kenan daga cikin abinda za mu iya kawowa al’umma dangane da amfanin itaciyar nan mai tarin albarka ta Baure ( Teen).

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullubemu da RahamarSA.🤲🏻)

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »