*
Ka samo kwallon mangwaro da yawa ba sosai ba, sai ka yayyanka su gusti-gutsi sai ka shanya su a rana wuri mai tsaftata , idan ya bushe sai ka daka shi ko ka nika shi (yazama gari yayi laushi sosai.)
Kadan daga cikin amfaninsa shi ne:
1- Yana magance matsalar ASTHMA da Yardar Allah wannan mujarrabi ne sosai DA YARDAR ALLAH. ( Idan aka sanya cokali daya na garin a cikin kofin ruwan zafi za a iya sanya zuma daidai kima ayita motsawa har ya garwaye ko ya jiku sosai, sai a rika sha sau daya a rana har tsawon sati 3 zuwa 4.)
2- Yana magance matsalar cin kasa da wasu yaran ke yi DA YARDAR ALLAH. (Idan ana zuba garin kamar karamin cokali a cikin ruwa normal ana baiwa yaran suna sha da ruwa.)
3- Garin Mangwaro idan ana sanya cokali daya a cikin kofi daya na ruwan dumi kullum da safe da daddare ana sha, yin hakan: Yana tace sugar din dake cikin jini, kuma yarage karfin cutar Diabetics, Kuma yana daidaita jini ga masu fama da matsalar hawan jini, Da YARDAR ALLAH.
4- Masu fama da matsalar Fibroids sai su samo kwallon mangwaro guda 10 su tsaftace shi sai su tafasa shi da ruwa kamar 2 Ltrs tsawon mintuna 20 zuwa 30 (za a iya sanya zuma daidai kima) sai a rika shan kofi daya da safe kofi daya da yamma har tsawon sati biyu. Za kuyi mamakinsa da Yardar Allah.
Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.
Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.
(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)