Yadda Za Ka Magance Matsalar Kaushin Kafa Da Man Wanke Baki (Maclean)

0 393

Idan har kafarka tana yin kaushi ko tauri ba ta yin laushi/taushi musamman ma a irin wannan yanayi na sanyi da ake ciki, to ga mafita nan da yardar Allah.

Abubuwna da za ka samo kawai su ne kamar haka:

1- Maclean/ Toothpaste ( Man wanke baki).

2- Sugar ( fara Wacce dai ake sha).

3- Man Zaitun mai kyau.

4- Man Ridi/Kantu ( Sesame/ Simsim Oil )

Yadda ake amfani da su shi ne kamar haka:

Za ka matse Maclean dinne kamar adadin cokali 2 a cikin wata roba ko kwano, sai ka sanya Sugar baban cokali 1 a cakudasu da kyau, sai a sanya Man zaitun babban cokali 1 sai a cakuda su da kyau.

Idan an kammala sai a samo brush irin wanda ake wanke baki da shi a rika dangwalo wanna hadin ana shafawa ana gogawa a kafar har da tafin kafa inda kaushin yake a hankali cikin natsuwa, bayan an kammala ne sai a samo rapper wadatacciya (ledar nan mai ash-color wacce ake rufe abu da ita), sai a rufe kafar tsawon mintuna 20.

Bayan ya cika mintuna 20 din sai a cire ledar a samu tawul ( Towel) a goggoge kafar da kyau, sai aje a wanke, in sha ALLAH za kuji dadin wannan hadin, Sai da dare kuma arika shafa man Ridi/Kantu (Sesame Oil) a kafar sai a sanya Safa arika kwana da ita, idan har ana yinsa akai akai.

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.

)

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »