Yadda Zaku Kawar Da Warin Hammata  

0 381

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Wurin hammata lalura ce da kan damu mutane dayawa musan man Mata a yanayin zafi saboda rashin samun wadatacciyar iska ko kuma kasancewar aikace aikacen cikin gida. Akwai magunguna dayawa na Hausa da ake amfani da su don kawar da wannan wari amma a ciki mun duba kayan da mata sukafi amfani dasu a kitchen domin su samu sauki.

BAKING SODA

Baking Soda na taimakawa matuka wajen saurin kawar da warin hammata nan take ga namiji ko mace, kawai zaku nemi cokali biyu na Baking Soda da kuma cokali daya na ruwan Lemon Tsami.

Zaku hade su sai ku dunga gogawa a wurin zuwa wasu yan mintuna sai ku wanke. Wannan hadi zai taimaka sosai wajen kawar da warin.

TUFFA

Zaku samu Tuffa dinku sai a nikata kusamu ruwa  kadan sai ku zuba a juyashi sosai sai a samu yadi ko auduga  a dinga tsomawa  ana sawa a Hammata a matse har zuwa mintuna 10 zuwa 15. Sai a cire ayi haka kullum za’a rabu da warin hammata.

RUWAN DANKALIN TURAWA

Wannan yafi kowanne, wajen kawar da warin hammata, zaku samu katon Dankalin Turawa sai ku nikashi a Blender idan yayi saiku matse ruwan nasa a wani wuri sai ku dinga wanke Hammatar taku dashi.

Ko kuma ku samu Dankalin Turawan kuyanka sala sala saiku dinga go gawa a hammatar taku zuwa wani lokaci kadan shima hakan zaisa warin ya fita nan take.

RUWAN TUMATUR

Kisamu Tumatir naki masu kyau ki jajjaga ruwan ya fita sai ki hadasu da ruwan Lemon tsami ki dinga gogawa a Hammatar har na tsawon mintuna goma shima zai kawar miki da warin hammata.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »