Amfanin Dafa Da Shan Bawon Abarba Da Ganyen Darbejiya Ga Lafiya.

0 310

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Idan har yaranku na fama da Malaria kuma ana ta basu maganin malaria amma har yanzu shiru babu wani sauki ko sauyin da ake gani a jikin yaran game da Malaria din.

Tabbas duk Zazzabin Malaria din da ba’a iya shawo kanshi cikin lokutan da suka kamata ba, zai iya haifar da cutar ANEMIA da JAUNDICE ( Cutar da take sanya jiki ko fatar jiki tayi yellow ko kuma idon yayi fari) saboda rashin wadataccen jini da kuma rashin sinadarin red blood cell. Kuma idan har akayi wasa da lamarin ciwon zai iya zama mai wuyar sha’ani kuma zai iya sanya Qoda (Kidney) ta samu matsala, za ta iya taba hankalin mutum ko kuma ta iya zama sanadiyyar rasa rayuwar yaro.

MENENE MAFITA YANZU?

Idan har ana so a magance wannan matsalar tun farko kafin tayi tsamari to ga abinda yakamata nan asamo wadan nan abubuwan :

1- Ganyen Darbejiya/Maina/Bedi guda 20.

2- Bawon Abarba daidai qima.

3- Ruwa 2 litr.

YADDA ZA AYI MUSU SHI NE:

A wanke su da ruwa mai kyau kuma mai tsafta, sai a tafasa su tsawon mintuna 10.

-Yara yan Shekaru 2 zuwa 3 za su rika shan babban cokali 2 safe da yamma.

– Daga shekara 4 zuwa 5 za su rika shan babban cokali 3 safe da yamma.

– Daga shekara 6 zuwa sama za su rika shan cokali 5 safe da yamma.

A aikata haka har tsawon sati daya… Sai ka dakata ka bayar da tazarar kwanaki 7 sai ka kara sha na tsawon wani sati daya…. Idan har kayi wata daya kana aikata haka, ina mai tabbatar maka cewa da YARDAR ALLAH za ka nemi maleria ka rasa a jikin ka.

Kowa zai iya sha banda mace mai ciki da mace mai shayarwa.

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »