Fatima Lawal Aliyu wanda aka fi sani da (Tasalla Nabulusi), ana haifeta a garina Kano Unguwar Hausawa dake galadanci tayi karatun ta na Primary a Dan Dago sannan tayi karatun Diploma a bangaren Hadith a kwalejin ilimi ta Aminu Kano wato Legal ta kumayi advance Diploma duka a Makaranatar.
Taci gaba da karatun litattafan Addinin Islama a wurin Mahaifin mijin ta, bayan da mahaifin mijin ya samu lalura sai ya hada ta da wani malamin domin cigaba da koyan wasu Litattafan Musulunci har ta samu Alqur’ani da kuma tafasirin sa .
Ta shafe shekaru sama da ashirin tana tafsirin Alqur’ani mai girama, kuma ta horar da wasu dayawa. Sun bude makarantun Islamiyya inda a nane suke koyar da Mata ilimin Addini iri daban daban.
Ta fara koyarwa a wasu Islamiyoyi tun tana yar shekara 10 a Duniya wannan dalilin yasa bayan Aurenta suka bude islamiyoyi a ciki da wajen garin Kano don ilmantar da mata Ilimin Adnin Musulunci dana zamantakewar Aure. Ta shaidawa manema Labarai irin gwagwarmayar da tasha wajen koyar da mata ilimin addnin musulunci dana zaman takewar Aure. Sannan Makarantar su na daya daga cikin Makaranta a Jihar Kano da suka fara assasa sanya Hijabi ga Mata, wanda hakan har ya janyo raguwar mata a makarantar.

Sannan a cikin gwagwarmayar ta samar da ilimi ga mata sunkan shiga kauyika don su Musuluntar su kuma koyar da Ilimin Addini, harma akan jefe su da Dutse a wasu kauyukan.
Ta shaidawa manema labarai cewa kasancewa koyarwar da take tasamu dukaka iri daban daban, harma iyayen mijinta basa iya fadar sunan ta saboda girmamawar da suke mata.
Sannan ta shaidawa manema labarai cewa yawancin tambayoyin da tafi samu daga wurin mata sune akan Aure, wanda hakan yasa Mata ke ganin cewa tafi kwarewa wajen war-ware matsalar Aure.
An kuma tabaye ta Shekarun Aurenta tace anyi shi 1 ga watan Janairu shekarar alib 1979 shekaru 44 da yin Auren, kuma tana da ‘ya’ya 11 rayayu Maza 5 Mata 6 wasu kuma a ciki ‘yan Biyu ne. sannan tana da jikoki guda 27 biyu sun rasu 25 suna raye. Kuma ita kadai Mijinta ya Aura.
Allah ya karawa Malama Fatima Lafiya da Nisan Kwana Amin.