Amfanin Rose Water 10 Ga Lafiyar Jikin Dan Adam

2 773

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Rose water an dade ana amfani da shi tsawon zamani a doron kasa a muslunce da kimiyyance akwai tarihi me tarin yawa akan amfanin shi, saboda amfanin shi (rose water) wajen karfin warkar da cutukan fata da lemanta jiki, sabunta jiki da kara masa sheki da dame fatar data fara yaushi.

Rose water ruwan fure ne wanda ke dauke da wani sinadari da ake kira (Fifi) wanda ake amfani da shi a kusan dukkanin wasu mayukan bature da ake yi a wannan zamanin na gyaran fata. Ga kadan daga cikin amfanin Rose water.

Rose Water
Rose Water
 1. Rose water yana gyara fatar data yamushe ta hanyar kara shi a cikin man shafawa na yau da kullum.
 2. Rose water yana da sinadaran maida tsohuwa/tsoho yarinya ta hanyar saka annuri, nishadi da yawaitar murmushi a fuska.
 3. Ana amfani da Rose water dan tada komada (make up over) idan aka hada shi da man kwakwa ana goge jiki (cleanser).
 4. Ana kara Rose water a turaren jiki (body spray) dan dadewar turaren a kan fata.
 5. Ana zuba Rose water a hadin turaren humra na amare dan kaucewa saurin fahimtar canzawar fatar jikin amarya musamman nono, hips, da tumbi sakamakon canzawar cimakar gidan miji.
 6. Ana hada Rose water da zaitun original ana shafe jikin da yake yawan bushewa musamman lokacin sanyi.
 7. Rose water yana rage matsalolin depression da anxiety idan ana sha lokaci lokaci.
 8. Masu maikon fata da gishirin fuska ana hada Rose water da khaltuffa ana shafawa da dare da safe a wanke.
 9. Ana wanke baki da Rose water dan kashe kwayoyin cuta, warin baki da hasken hakora.
 10. Ana hada Rose water da man shanu da man zaitun dan gyara gashi lausasa shi, sheki da kara yawan shi.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

 1. ABDURRASHEED YAKUBU SHALL says

  Good

 2. Musab says

  Masha Allah gsky naji dadin ynd kk tai makama alumma Allah qara basira.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »