Amfanin Cin Dabino Ga Lafiyar Jiki

0 442

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

DAGA CIKIN AMFANIN CIN DABINO DA SAFE KAFIN A YI BREAKFAST

1-Yana warware matsalar fitar fitsari cikin ikon Allah.

2- Yana tsaftace Hanta kuma ya wanke Qoda.

3- Yana da amfani ga masu fama da ciwon tari ko wane iri ne kuwa da sauran cutukan kirji.

4- Yana kara jini mai kyau a jikin mutum.

5- Yana da matukar amfani ga masu fama da ciwon baya.

6- Idan aka daka shi akayi garinsa ana zuba cokali 2 a nono ko madara ( ta gari ko ta ruwa) ana sha, yana matukar amfani ga lafiyar ma’aurata maza da mata domin yana karfafar kowanne a cikinsu.

7- Garinsa idan ana sha da Nono ko madara ( ta gari ko ta ruwa) safe da dare da ruwan zafi kadan yana matukar amfani na bammamaki ga masu fama da matsalar low sperm count.

8- Yana lalata SIHIRI kowane iri ne a jikin mutum Idan har ana cin guda 7 kullum da safe kafin ayi breakfast har tsawon wata 2 ko kwanaki 60, kuma da yardar ALLAH jikin ka zai samu tsari daga kamuwa da wani nau’in sihiri, Kambun-baka ko hassada kenan har abada sai dai wani Ikon Allah.

“Mu sani cewa: Masu fama da cutar SIHIRI ko shafar jinnu matukar sun dage da yiwa ANNABI SALATI cikakken salati ba adadi kuma a kullum kuma a ko da yaushe, ina tabbatar muku za ku rika ganin sauyi a jikinku na bammamaki da yardar Allah, domin SALATIN ANNABI SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA yana matukar takurawa Shedanun Aljinun dabba mutane.”

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »