Bani Da Lafiya Kashi Na Sabain Da Uku (73)

0 515

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

“Tun kuna dauke da cikin yaranku yakamata ku rika nemar musu kariyar Allah daga sharrin dukkanin halittunsa, saboda sau da dama daga nanne ake fara yiwa yara illa har girmansu, abu kuma yazo yana kokarin gagarar Kundila. Allah ya kyauta”

Malamin yana kammala fadin haka ne sai can akaji wata sallama daga layin baya ana cewa: Assalamu alaikum Mallam, shin zan iya yin tambaya a wannan gabar kuwa?

Kowa ya waiga yana so yaga shin wacece wannan mai son tayi tambayar nan kuwa.

Sai Ummu Labeeba taganta tace: Au ashe ma Maman Walidi ce.

Ummu Bareerah ta tambayi Ummu Labeeba tana cewa: Au dama kin santa ne?

Ummu Labeeba: Kwarai kuwa makobciyar mu ce wallahy, saboda ta yi haihuwa wajan 3 amma duk yaran da nakasa ake haifar su, wani kiga kafarsa a shanye, wani kuma yawu yayita dilala, ga shi kullum yaran cikin rashin lafiya, gaskiya kam tana fama wallahy.

Ummu Bareerah: Allah sarki, Allah yabasu lafiya kuma yakara tsaremu da su baki daya.

Sai Malamin yace: Na’am, ba matsala kina da damar yin tambayarki malama.

Sai Maman Walidi tace: Yauwa Mallam ina godiya Allah yasaka da Alkhairi. Mallam mun saurari bayananka kuma mun gamsu sosai sannan muna godiya tare da Addu’ar ALLAH yasaka da Alkhairi. Amma ni tambayata anan itace: Shin wane mataki ne yakamata mu iyaye mata mudauka ga yaranmu kanana da ma wadanda muke dauke da su a cikinmu kafin mu haife su, domin samun kariyar ALLAH YAkaremu da su daga sharrin dukkanin halittunSA?

Ummu Labeeba ta kalli Ummu Bareerah sai tace: Wato matar nan fa ta yi muhimmiyar tambayar kuma wacce mata da yawa muke buƙatar muji amsarta tun ba yau ba wallahi. Alhamdulillah.

(Insha ALLAH a rubutu nagaba za muji abinda mallam zaice.)

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)

Domin karin bayani:
👇👇👇

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »