Bani Da Lafiya Kashi Na Sabain Da Biyu (72)

0 532

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Malamin yace : Mafita anan kala biyu ce, na farko akwai Riga-kafi (neman kariyar Allah kafin abin ya faru da mutum har yayi tasiri akanshi) sai kuma yin maganin da bai sabawa Shari’ar Allah ba idan abin yafaru har yayi tasiri akan mutum.

Kowa a cikin dakin taron sai da ya gyara zama kuma suka kasa kunnuwansu cikin nutsuwa suna sauraron abinda mallam zai ce.

Bareerah ta kalli Labeeba tace: Ikon Allah, wato yar uwa kinga yadda dakin taron nan kuwa ya kara yin tsit akan wannan mas’alar da za a tattauna akai?

Labeeba : Ai ke kuwa dole yayi tsit mana, saboda lamarin nanne ya addabi kowa, kuma ana son samun mafita irin wacce ta dace da shari’ar Allah, to sakamakon wasu sun afka hannuwan miyagun masu magani suna ta cin kudadensu kuma suna hallakar da su, su raba su da Imani, duk da sunan maganin tsarin jikin yara ko kau-da-bara da dai sauransu.

Bareerah: Kaico…Allah ya kyauta kuma yakara tsare mana imaninmu. Amma bari dai mu ma muji bayanin domin na tabbata zamu karu daga abinda mallam zai furta mana.

Malamin yaci gaba da cewa: Ai wato da farko dai za mu dau bayani akan Riga-kafi saboda shi ne na farko kuma wanda yakamata mu kiyaye musamman ma ga yaranmu manya da kanana da kuma jarirai har ma da waɗanda suke a cikin ciki wadanda ba a haifesu ba.

Mai gabatarwa: Au mallam kana nufin ma yanzu har wanda ba a haifa ba ma yana bukatar ayi masa riga-kafin kamuwa da sharrin Hassada, Kambun-baka da kuma sharrin sihiri na Mayu da yan kungiyar asiri?

Malamin: Kwarai kuwa ai wanna ma shi ne abinda yafi dacewa saboda wata matsalar shedanun ma tun yaro yana cikin cikin mahaifiyarsa yake gamuwa da ita har ya fito yana fama da ita a rasa me ke damunsa nan kuwa matsalar lalurar hassada ce da Kambun-baka ko kuma shafar jinnu.

(Insha ALLAH za muji ci gaban a rubutu nagaba.)

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »