Amal Umar na daya daga cikin yan wasan kwaikwayo na Kannywood, An haifeta a ranar 21 ga watan Oktoba shekarar alif 1978 a garin Katsina.
Amal tayi karatun na Primary da sakandare duk a garin na katsuna, sannan tayi Diploma a Maitama Sule University.
Amal Umar ta fara fitowa a kannywood ne a shekarar 2015, lokacin da ta shiga masana’antar a matsayin mawakiya kuma ta fara fitowa a faifan bidiyo tare da manyan mawakan kannywood irin su Umar M Shareef, Garzali Miko, Hamisu Breaker, Musbahu Anfara, da sauran fitattun jarumai.
Amal Umar ta fara fitowa a fim dinta na farko a cikin fim din “Gidan Abinci.” Fim ɗin da ya fara ɗaukaka Jarumar.
Ta yi fice ne bayan ta fito a cikin fim din “Mujadal” wanda jarumar ta samu lambobin yabo da dama.