Bani Da Lafiya Kashi Na Arbain Da Hudu

0 527

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Abu Ruwaihah: Ai ALLAH ya basu haihuwar mana, saboda yakara musu wata jarabawar akan wacce suke cikinta.

Ummu Arqam tayi murmushi tana cewa: Na san yanzu su za su ga cewar kamar shi Bokan ne yabasu haihuwa har su rika jinjinawa aikinsa, nan kuwa basu san rabonta ne ya tsaga ba, dama can ALLAH ya qaddara za ta samu haihuwa a lokacin da ta haihun, amma komai fa sai da amincewar Allah, wawayene kawai ba sa gane hakan.

Abu Ruwaihah: Ai dama yawancin mutane ba sa ganewa, haihuwar nan da suka samu da ma can Allah ya rubuta za su haihuwa a lokacin, amma sai suka bi hanyar da bata dace ba suka samu haihuwar itama cikin yardar Allah.

Abu Arqam: Yanzu ka ga rashin hakuri da kwadayi ya kaita da iyayenta ga aikata haramun, da ace sunyi hakuri basu turata ta aikata fasikanci da bokan nan ba, matukar tana da rabon haihuwar na tabbata za ta samu haihuwar. Allah dai ya kyauta.

Abu Ruwaihah: Yanzu ka ga ta samu haihuwar amma sai da-na-sanin samun haihuwar take ita da iyayenta saboda komai ya dagule musu, lissafinsu ya ki fitar musu da bahasi, mafarkinsu ya kasa tabbata, saboda yanzu maganar nan da nake muku asirinsu ya tonu, tuni Alhajin ya sallameta gaba daya.

Abu Arqam: ALLAH Sarki…. Ai ka ji irinta ko! Tun a duniya sakamako ya fara tabbata kuma da ma ai ramin karya kureshi ake yi, sun zo su maqalawa Alhaji Dan da ba na shi ba Dan gaba da Fatiha amma Allah bai yarda ba, sai suka wuce da kayan laifinsu da kuma tulin kayan kunya.

Ummu Arqam: Ka ga yanzu wannan ya zama darasi kenan ga sauran mutanen da suke da irin zuciyar wadan nan iyayen wajan son samun haihuwa ta ko wane irin hali kawai saboda a samu gadon Alhaji. To yanzu malam su din suna ina kenan?

Abu Ruwaihah: Ai tuni sun ma bar unguwar, saboda kowa ya san abinda ake ciki, ko wane lungu da sako batun kawai ake yi, abin duk ya ishe su shi ne suka bar unguwar gaba daya.

ABIN LURA

“Lallaikam, wannan shi ne gani ga wane ya ishi wane tsoron ALLAH, domin kadan kenan daga cikin sharrin ingiza mai kantu da bokaye ke yiwa mutane musamman ma mata, amma har yanzu da yawa ba sa ganewa. ALLAH yakara shiryar da mu hanya madaidaiciya .”

(Insha ALLAHu a rubutu nagaba za muji ci gaban bayanin.)

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »