Bani Da Lafiya Kashi Na Arbain Da Biyar (45)

0 455

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

ABIN LURA

“Duk abinda kaga ka nema a wurin ALLAH har kayi Addu’a ka bi duk wasu qa’idojin da shari’ah ta tanada wanda yakamata abi na ladubban yin Addu’a amma kaji shiru, to ka sanya yaqinin ALLAH ya karbi Addu’ar ka Insha ALLAHu. Hakuri kawai za kayi na jiran lokaci, ko kuma ALLAH ya sauya maka da abinda yafi wanda ka roka din alkhairi.”

Abu Arqam: ALLAH ya kyauta kuma yakara tsare mana imaninmu sannan yakara mana hakuri wajan jurewa duk wata jarabawar wacce za ta sanya ALLAH ya daukaka darajarmu. Wato mallam mu dangane da bayanin mu ya ake ciki kenan game da tambayoyin da kace za kayi mana?

Ummu Arqam: Eh kwarai kuwa, saboda dai yanzu kam mun karu sosai game da wadan nan bayanan mutanen da ka labarta mana, muna kara godiya sosai, domin yanzu ka ga zuciyoyinmu sun kara samun nutsuwa akan Tauhidin ALLAH ne kadai mai iya bayar da haihuwa ba waninsa ba.

Abu Ruwaihah: Ai ina sane da ku, kawai na kawo muku wadan nanne don Zuciyarku takara samun nutsuwa akan cewa komai sai ALLAH ya yarda kuma babu abinda ake yi a bayan ganin ALLAH, saboda Ilimin ALLAH da jinSA da ganinSA yana kewaye da kowa da komai da ko ina a fadin duniyar nan, ta yadda babu abinda zai iya buyar maSA.

Abu Arqam: Tabbas kuwa mallam, wannan batu haka yake, ALLAH yakara tsarkake mana zukatanmu da harsunanmu da kuma gabobinmu baki daya. Ameen ya Rabb.

Ummu Arqam: Na’am Mallam ALLAH yasaka da mafificin Alkhairinsa, kai muke sauraro.

Abu Ruwaihah: Wato dangane da irin matsalar nan, ana iya yiwa mutum sihiri ta yadda Boka zai kulla sihirin wajan wakilta Shedanin da yake tare da mutum wanda ake ce masa (Qareeni), wajan zama a mahaifar mace tayadda zai rika lalata duk wani ruwan namiji da ke iya shiga cikin mahaifar mace da ke yin sanadin ALLAH ya samar da haihuwa, ko ya toshe “Fallopian tube” ko ya sanya wani qari a mahaifarta sai ruwan ya kasa zama a mahaifar, tayadda idan taje tsarki bayan gama saduwa da mijinta sai dai taga ruwan ya biyo ruwan tsarkin ya fito waje ya ki shiga mahaifar.

Ummu Arqam: Subhanallah , Wa Laa haula walaa quwwata illa biLLAH !

Abu Ruwaihah: Ai ba su kenan ba, akwai wasu misalai da alamomin da za su kara fito muku da bayanin nan a fili Insha ALLAHu.

(Insha ALLAHu za mu cigaba da bayanin a rubutu nagaba)

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »