Da yawa daga cikin mutane ba su da masaniya kan amfanin da gyada ke yi a jikin mutum, Wasu mutane sun cewa cin gyada danya, dafaffe ko kuma soyayya na kara kiba a jiki sannan yana kawo wasu kuraraji a fuska wanda ake kira da ‘Pinples’.
A wannan rubutu zamu kawo muku muhimmancin cin gyada ga lafiyar jikin dan adam
- Gyada na ƙara girman jikin mutum musamman yara domin yana dauke da sinadarin ‘Protein’.
- Gyada na gyara fatar jikin mutum da hana saurin tsufa saboda kasancewar sinadarin ‘vitamin E’ a ciki.
- Gyada na kare mutum daga kamuwa da cutar bugawar zuciya.
- Gyada na dauke da sinadarin ‘vitamin B3’ wanda ke taimakawa wajen hana mutum mantuwa.
- Gyada na dauke da sinadarin ‘Phylosterols wanda ke kare mutum daga kamuwa da cutar daji.
- Gyada na kare mutum daga kamuwa da cutar suga.
- Ana samun sinadarin ‘Folate’ wanda ke bunkasa kiwon lafiyan mata masu ciki.
- Gyada na kara karfi a jiki.
- Gyada na sanya farin ciki ga mai cinya musamman masu yawan fushi.