Bani Da Lafiya Kashi Na Arbain Da Takwas (48)

0 624

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

ABIN LURA

“Ayoyin Alqur’ani da ingantattun Addu’o’i da Azkaar wadanda suka tabbata a sahihan Hadisan Annabi Sallallahu alaihi Wasallama da kuma wasu ingantattun hanyoyin da magabata na kwarai suka yi bayaninsu waɗanda babu guluwwi ko kuma cakuda karya da gaskiya balle shirka a cikinsu, su ne kadai hanyoyin da suke raunata duk wani qulli da makiricin shedanu kuma su lalata su tare da korar shedanun.”

Abu Ruwaihah yace: Wato iya wadan nan bayanan Insha ALLAHu idan kuka rike su kuma kukayi amfani da maganin nan da na baku a matsayin silar da Allah zai iya baku lafiya, ina kyautata zaton za suyi muku amfani kwarai da gaske.

Bayan da Ummu Arqam da Abu Arqam suka gama jin kadan daga cikin shawarwarin da Abu Ruwaihah yabasu sai Ummu Arqam tace: Alhamdulillah, wato Mallam muna godiya kwarai da gaske ALLAH yasaka da alkhairi.

Abu Arqam suka yi sallama da Abu Ruwaihah yayi musu fatan ALLAH yasa a dace.

Bayan wasu kwanaki Labeeba suna zaune ita da Ummu Labeeba a cikin gida sai Labeeba take cewa: Umma, Wata rana ina kan hanyata ta zuwa makaranta a cikin daidaita sahu (Napep) sai muka gamu da wata wacce muke zuwa karbar magani da ita a wajan Abu Ruwaihah mai suna Huda, kuma kinga matsalar mu daya ce da ita amma ita yanzu har ALLAH ya sa ta yi aure abinta.

Ummu Labeeba: ALLAH Sarki, ai ikon Allah kenan, kuma kinga a irin haka kar kije ki sanyawa kanki wata damuwa ta dabam, saboda komai da kika gani yana da lokacinsa, kuma yadda Allah yakawo mata karshen wannan lalurar ke ma ina kyautata zaton Allah zai kawo miki karshen ta ki lalurar, kawai abin bukata anan shi ne mu daage da yin Addu’a tare da hakuri abisa jarrabawar da Allah yake mana.

ABIN LURA

“Ina ma ace yawancin iyaye mata za su zama tamkar Ummu Labeeba a wannan fannin, wajan rarrashin diyansu mata akan matsalar da suke fuskanta ta jinkirin samun mijin Aure, ai kam da al’umma ta samu nagartattun manyan gobe. Amma abin takaicin sai kaga wasu iyayen ne ma ke hassala yaransu ko kuma su nuna musu muggan hanyoyin da zasu je su salwantar da mutuncinsu da kuma Imaninsu.” ALLAH ya kyauta.

(Insha ALLAHu za muji ci gaban bayanin a rubutu nagaba.)

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »