Bani Da Lafiya Kashi Na Arba’in Da Bakwai (47) Shawarwari Ga Ma’aurata.

0 563

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Ummu Arqam tayi ajiyar zuciya take cewa: Subhanallah ! Wato mallam cikin abubuwan nan da ka lissafa gaskiya ina fuskantar wasu da yawa daga cikinsu, sai dai fatan Allah yabamu mafita mai amfani.

Abu Arqam shi ma yace: Tabbas nima ina fama da matsalar nan. Allah ya kyautata mana kuma yasa mudace.

Nan take Abu Ruwaihah ya hada musu magani kuma yabasu wasu shawarari kamar haka:

1- Ku tabbata kunyi imanin cewa: ALLAH ne kadai zai iya warkar da ku ba wannan maganin da na baku ba, shi wannan maganin ba komai bane illa silar samun warakarku da yardar Allah, amma ba shi da ikon yin komai.

2- Ku dukufa wajan yin Addu’a ba dare ba rana, kuma ku rika sanya wasu ma suna yi muku Addu’a ( musamman wadanda kuke kyautata musu zaton mutanen kwarai ne).

3- Ku rika cika dukkanin farillan da Allah ya farlanta muku tare da yawaita yin nafiloli na Salloli da Azumi da kuma Sadaqa.

4- Ku tabbata kuna yin Azkaar na safiya da maraice, shiga toilet da fitowa, sanya tufafi da kwabewa, shiga gida da ficewa, cin abinci da gamawa da kuma ta saduwa da iyali.

5- Ku yawaita sauraro da karanta Alqur’ani Mai Girma musamman Surorin nan : Baqara, Nur, Yasin, Saffaat, Fussilat, Qaf, Jinn, Buruj, Kafirun, Ikhlas, Falaqi da Nasi.

6- Kar ku kuskura ku rika kwanciya bacci ba tare da alwala ba, ko da mace ba ta Sallah to tayi alwalar kwanciya bacci ( saboda tsaro).

7- Ku rika mu’amala da Man Zaitun, idan da hali ma ku rika sanyawa a cikin abincin ku, shi da man kwakwa da Man Ridi, saboda sun da Amfani matuka a cikin jikin Dan Adam a irin wannan yanayin, kuma dukkanin su an tabbatar da shedanun jinnu ba sa son su saboda suna takura musu.

(Insha ALLAHu za muji ci gaban rubutun a rubutu nagaba.)

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »