Muhimmancin Cin Ruman Ga Lafiyar Jikin Dan Adam

0 412

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Ruman yana cikin tsirrai masu matukar amfani a duniya wadanda masana sukay bincike a kansa.

Tun shekaru dubunnai da suka wuce ake amfani da Ruman a matsayin Magani a kasashen Gabas ta tsakiya wajen maganin Olsa da Gudawa da dai sauransu.

Allah Ya ambaci Rumman a Alqur’ani, cikin Suratur Rahman, lokacin da Yake bayyana irin bishiyoyi na alfarma da Ya tanada a ckin Aljanna.

Kasancewar Rumman yana cikin bishiyoyin Aljanna ya isa ya nuna mana muhimmancinsa ga rayuwar dan Adam kasancewar Aljanna gidan ni’ima ce.

Bincike ya tabbatar da cewa Rumman yana:

1. KARA LAFIYAR ZUCIYA.
Shan Ruman yana da muhimmanci sosai wajen kara lafiyar zuciya. Yana rage sinadarin ‘atherosclerosis’ wanda yana daga cikin sinadaran da ke haifar da cututtukan zuciya. Yana rage hadarin toshewar hanyoyin da ke kaiwa da fitar da jini daga zuciya zuwa kwakwalwa.

2. YANA RAGE KITSE MARAR AMFANI DA KUMA ƘARA MAI AMFANI.
Haka dai Rumman yana rage sinadarin LDL ko mu ce kitse mara amfani wanda ke cikin jini, sannan ya samar da sinadarin HDL wato kitse mai amfani.

3. DAI-DAITA SIKARIN JINI.
Ruman yana da sinadarin ‘fructos’ don haka baya kara adadin sikarin da ke cikin jini kamar yadda wasu tsirran suke yi. Masana sun yi bayanin cewa ba wani hadarin karuwar sikari a cikin jinin masu cutar diabetes wadanda suka sha Rumman kullum har tsawon sati biyu.

Ruman
Ruman

4. MAGANIN HAWAN JINI.
Ruman sananne ne wajen rage matsalar hawan jini.

Rage Hadarin Kamuwa da Cutar Kansa (cancer).
Shan lemon juice na Ruman kofi daya a kullum yana rage kwayoyin cutar kansa dake jikin mutum.

5. MAGANIN GUDAWA.
Shan Ruman tare da zuma cokali daya yana taimakawa wajen warware matsalolin da suka shafi Hanji. Kamar Gudawa, Atini, kumburin ciki da dai sauransu.

6. SAUKAKA FITAR FITSARI
Ga masu matsalar.

7. MATA MASU CIKI.
Ruman yana da sinadaran vitamins da minerals wadanda ke taimakawa mata masu ciki wajen hana yawan ɓacin ciki, ciwon kafa da haihuwar yara wadanda nauyinsu bai kai ba.

8. GYARA FATA.
Shan lemon Ruman yana gyara kowace irin matsalar fata. Yana maganin matsalar bushewar fata yana kuma samar da tattausar fata kuma lafiyayyiya mai kyau.
Shafa Ruman a fatar jiki yana maganin kuraje tare da ba ta kariya daga cutar Kansa.

9. ZUBEWAR GASHI.
Shan Ruman yana samar da wasu sinadarai a jikin mutum wadanda ke hana gashi karyewa da zubewa.

10. RASHIN SHA’AWA.
Shan lemon Rumman yana maganin matsalar rashin sha’awa ga ma’aurata. Yana kuma Kara Kafin Maza.

11. RASHIN HAIHUWA.
Amfani da Rumman na taimakawa wajen maganin matsalolin da kan iya kawowa mutum rashin haihuwa.

12. KARFAFA GARKUWAR JIKI.
Shan Rumman na taimakawa masu cutar Raunin Garkuwar Jiki kamar HIV aids wajen kara karfafa garkuwar jikinsu.

Daga Shafin Sunnah Medicine,

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »