Bani Da Lafiya Kashi Na Hamsin (50)

0 521

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Nan take dai Salaha ta kara fahimtar fa Ummu Labeeba ba lallai ne ta karbi tayin da take yi mata ba, sai ta mike tayi musu sallama ta fice abinta.

Bayan fitar ta ne ita kuma Labeeba na gefe sai take cewa: Wato Umma wai ita matar nan ko tsoron Allah ma ba ta ji, a irin maganganun nan da take fadi?

Ummu Labeeba: Hmm yoo ai dama duk wanda ya biyewa tafarkin Shedan za ki ga kullum ba shi da wani aiki sai na Shedan din, ba ruwansu da jin tsoron Allah balle jin kunyar mutane.

Labeeba: Tab dijam, Allah yakara tsare mana imaninmu kuma ya tabbatar da mu akan tafarkin Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama har abada. Ameen.

Washe gari Labeeba tayi shirin tafiya makaranta, sai Abu Labeeba ke ce mata: Ki tabbata dai kinyi Addu’ar fita gida, kuma idan anje makarantar kisan abinda yakaiki makarantar ba shirme da shiririta ba, kuma kar ki yarda ki biyewa shedancin matar nan Maman Sultan.

Labeeba tayi mamakin yadda Abbanta yasan Maman Sultan, sai take tambayarsa tana mai cewa: Abba, ashe kai ma ka san Maman Sultan kenan?

Abu Labeeba: Kwarai kuwa, ai nima jiya ne naji wasu ke labarta min cewa : Matar a makarantar ku take, tana hulda ne da bokaye da malaman tsubbu, tana kawo musu kwastamomin yan mata da zawarawa da kuma matan Aure, shi yasa yanzu da yawan yan mata basu da wurin zuwa sai wurin bokaye wai da zummar ayi musu aiki akan samarinsu ko wadanda suka jima basu yi aure ba, da matan Aure masu neman haihuwa ido rufe.

Ummu Labeeba: Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un, wai yanzu ma har makarantu wannan bala’in ke bin yan mata da zawarawa da kuma matan Aure ?

(Insha ALLAHu za muji ci gaban bayanin a rubutu nagaba.)

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »