Naziru M Ahmad wanda akafi sani da Sarkin Waƙa na daya daga cikin shahararrun mawakan kannywood da kuma Jihar Kano baki ɗaya, haka kuma yana ɗaya daga cikin manyan masu shirya finafinan Hausa masu dogon zango da ake gabatar wa a gidan talabijin na Arewa24.
Naziru M Ahmad wanda aka fi sani da Sarkin Waƙa an haife shi a Gwammaja a ranar 4 ga watan Satumba shekarar alif 1986.
Naziru ya samu sarautar sa ta Sarkin Waƙa ne yayi da yayi wa Sarkin Kano Muhammadu Sunusi na II Waƙa, wanda aka naɗa shi Sarkin Waƙa a ranar 17 ga watan Disambar shekarar 2018.
Sarkin Waƙa ya fadi irin soyayyar da yake yiwa jaruman wakokin Hausa irinsu Mamman Shata, da Dankwairo. Kuma ya shaida ba zai iya cewa ga abin da ya ja hankalin sa ga waka ba, amma yayi mafarki zama mawaki ne tun yana ɗan shekara bakwai, kuma ya fara waka ne a lokacin da babu wurin yin Waƙa a Kano, ya kanyi waka a gaban jama’a harma a yanke shi.
Naziru ya shiga harkar waƙa gadan gadan a shekarar ta 2000. Yayi waƙoƙi da dama kamar su:
Musa Jidda | Lamido |
Sabon Sarki | Wasiƙa Ga shugaban Ƙasa |
Sunusi Lamido | Mata Kudau Turame |
Mati Da Lado | Dallatun Zazzau |
Matar Jami’a | Jarman Wudil |
Ado Bayero | Wani Gari |
Ahmad Musa | Yata Fadimatu |
Dan Giya | Gangar Jikinta Na Aura |
Wani Gari | Sardaunan Samaru |
Sunusi Na Biyu | Sardaunan Samaru |
Hanyar Kano | Murnar Sabon Sarki |
Kanin Muji | Sardaunan Gora |
Umar Turawa | Ba Mutum Bane |
Abdulhalim | Usman Zannuraini Musa Jidda |
Na’iman Da’iman | Sultan Biyamin Sarkin Das |
Muhammad Rahman | Ghazali Maitama and Farida Chanchangi |
Kuliyan Zazzau | Umaru Ahmad and Hadiza Abdallah |
Haka zalika Sarkin waƙa nada aure har da ya’ya huɗu.
Thanks you all