Amfanin Ganyen Lansir Ga Lafiyar Jiki

0 1,222

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Lansir daya ne daga cikin ganyayyakin da wasu da yawa ke amfani da shi a fannoni da dama, musamman ma a tafasa shi a rika sha kamar Tea, ko a yayyanka ganyen a sanya a abinci arika ci da dai sauransu.

Wasu na amfani da shi ne kawai ba tare da sanin tarin amfanin da yake da shi a jikkunan da lafiyar mu ba. Tabbas Lansir abu ne da yakamata mu cigaba da amfani da shi, idan har kuma bamu taba amfani da shi ba, ya kamata mu fara amfani da shi saboda bincike ya tabbatar kuma ya nuna cewa: Yana da matukar amfani a jikin mu da kuma lafiyar mu.

YADDA AKE AMFANI DA SHI.

  • Za a samo ganyen lansir sai a wanke shi sosai a tsaftace shi sai a samo lemon tsami kadan a hada shi da ganyen Lansir ɗin, sai a zuba musu ruwa kofi 3 a ciki, a dora a kan wuta abarshi yakai mintuna 30 sai a sauke kuma a tace, sai a sha kofi 2, tsakanin shan kofi na farko da na 2 a bar tazarar akalla mintuna 15.
  • A samo ganyen Lansir sai a tsaftace shi a cire duk wani ganye wanda ba kore ba a jikinsa, sai a yayyanka shi a zuba masa ruwa kimanin kofi 2 sai a tafasa shi, idan yatafasa sai a sauke shi a barshi yayi mintuna 5 bayan ya huce sai a tace shi a rika shan kofi 1 kullum da safe kafin aci abinci.
  • A tsaftace kuma ayayyanka ganyen Lansir din sai a sanya shi a tafasa da ruwa, sai a barshi ya huce kuma a sanya shi a cikin wuri mai sanyi kamar firjin da tayadda zaiyi sanyi ba sosai ba, sai a rika shan kofi 1 da safe 1 da yamma.

Ga Fa’idar Shan Wadannan Hade-Haden Na Lansir Da Muka Lissafo A Sama.

  • Yana daidaita jinin al’ada da izinin Allah.
  • Yana taimakawa masu fama da ciwon ƙoda da kuma Saifa.
  • Yana magance duk wata matsalar dake a mafitsara da izinin Allah, mace ce ke fama da ita ko namiji.
  • Yana kyautata numfashin mutum kuma yana taimakawa masu fama da ciwon Tari da Asthma (Asma).

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

ABIN LURA:
Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

Dan uwanku:
Idris M Rismawy (Abu Nu’aym)

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »