Amfanin Ruwan Kanzo Ga Lafiyar Jiki.

0 2,758

Ko shakka babu ruwan kanzo maganine, musamman ruwa kanzon tuwon gero ko na dawa da suka kwana a cikin tukunya suna jiqa wannan sabon maganine ga duk mutum dan shekara talatin zuwa kasa.

A can shekarrun baya iyayen mu mata idan suka kwashe tuwo sukan zuba ruwa a cikin tukunyar su kwana washegari a diba a kofi a sha akwai faidodi muhimmai na yin haka sai dai ba kowa ya sani ba.

Wannan yana maganin miyagun bakuna da mayu da kambun baka da miyagun Idanuwa na mutane da kuma dafin yawun miyagun bakunan da basa iya ganin abu su kyale.

A baya ga haka kuma ana hada Zuma da ruwan kanzon da suka kwana a cikin tukunya, ana tarfa Zuma mai kyau sai a sha tun kamin a karya.

Maganin :
Maganin rashin lafiyoyin da a ke tashi dasu yayin tashi daga bacci. Wanda zaka kwanta lafiya lau amma sai ka wayi gari da wata rashin lafiya na damunka a jiki. Wacce ake kira da turanci (alleviates common morning sickness)

Ana baiwa yara kamin su je makaranta zasu sha kamin su karya bayan mintuna talatin sai su karya, yana karawa kwakwalwa karfi na hadda da basira.

Mai yawan shan taba sigari shima zai iya sha zai rage mashi da wannan dafin daka iya illata ciki ko baya ga huhu. (reduces respiratory system disorders among tobacco smokers)

Mai kuraje a cikin ciki da kuma wanda ke jin zafi ko ƙuna a cikin ciki. (abdominal sores,stomach or internal heat)

Yawan ciwace ciwace, yau ciwo gobe lafiya, sai a tarfa Zuma mai Dan yawa a ciki a sha. (recurrent infections)

Maganin kuraje a kan harshe, da na cikin baki zuwa makogwaro (thrush, mouth and throat sores)

Yana Rage nauyi, ƙiba, da kuma tumbi ga masu nauyin jiki (weight management)

Idan kana fama da wata doguwar jinya a jiki sai ka sha da yardar Allah zaka samu sauqi (while on protracted illness)

Yana ƙara karfi ga garkuwar jiki (immune booster)

Rigakafin kamuwa da wasu cutuka a cikin gari.

Mai karamcin bacci da yawan damuwa (hallucinations and depression)

Rashin karfi da kuzari a jiki (vitality and energy drinks).

Kaikayin fatar jiki da kuraje ko babu kuraje (eczema)

Sanyin mura (cold and nasal congestion) sai a jefa citta a cikin ruwan kanzon su kwana suna jika da safe a tace a tarfa Zuma a sha.

Cutukan daji waton cancers. A nemi lemun zaƙi a tace ruwan kanzo a tafasa da kyau sai a sha.

ABIN LURA:
Kada a bari ƙanzon ya ƙone, idan ya ƙone baya maganin da ake buƙata kada kuma a bari sai ya bushe, da zaran an kwashe tuwo ake zuba ruwa masu kyau a ciki sai a rufe tukunyar sai gari ya waye ayi amfani dasu.

Ba a bukatar ruwan kowane abinci face na gero ko dawa.

DAGA Shafin Ciwo Da Magani

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »