Amfanin Ganyen Gwaba Ga Lafiyar Jiki

2 2,944

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Da yawa daga cikinmu suna cin Gwaba amma suna barin ganyen ba tare da tunanin amfanin lafiyar da ganyen ke da shi ba. Ganyen Gwaba ya ƙunshi manyan sinadarai kamar su Bitamin A da C, potassium, lycopene da fibre.

A cikin wannan bayani, mun jero wasu fa’idodin kiwon lafiya masu muhimmanci da ganyen gwaba yake waɗanda yakamata ku sani.

Cututtukan Zuciya:


Ana tafasa ganyen Gwaba asha don rage haɗarin cututtukan dake samun zuciya da bugun jini.

Lafiyar Kwakwalwa:


Yana taimakawa wajen kewayawar jini zuwa kwakwalwa Kasancewar akwai sinadaran bitamin B6 (pyridoxine) da B3 (niacin) da ake samu a cikin ganyen Gwaba.

Kariya Daga Cututtuka:


Shan shayin ganyen Gwaba yana taimakawa wajen haɓaka garkuwar jiki da rage haɗarin cututtuka dake jiki.

Sammar Da Ruwan Mani mai Haihuwa:


Ga maza masu matsalar rashin haihuwa ganyen Gwaba zai inganta samar da ingantaccen kwayoyin haihuwa ga maniyyi. Don haka, an ba da shawarar sosai ga mutanen da ke fama da matsalolin haihuwa dasu dinga amfani da shi.

Ƙara Sha’awar Jima’i:


Shayin ganyen Gwaba zai kara sha’awa a tsakanin ma’aurata. Zaku tafasa ganyen Gwaba sai a debi kamar kofi guda a saka zuma a dinga sha.

Rage Ciwo:


Ganyen Gwaba ya ƙunshi sinadarin quercetin wanda ke sa shi tasiri wajen rage ciwo da kawar da cututtuka.

Matsalolin Haila:


Shayin ganyen Gwaba yana da amfani ga mata wajen sauƙaƙa al’ada da ciwonta, da rashin gudanar jinin al’ada.

Rage nauyi:
Bugu da ƙari sinadaran quercetin da aka samu a cikin ganyen Gwaba yana hana samuwar ƙwayoyin kitse da catechin wanda ke da tasirin ƙona kitse a cikin jiki. shayin ganyen Gwaba yana hana carbohydrates rikiɗawa zuwa sukari don haka yana hana duk wasu kwayoyi da zai sanya ƙiba a jikin mutum.

Ciwon Ciki Da Wahalar Yin Bahaya:


Shayi na ganyen Gwaba yana da kyau na musamman ga kariya ga mafi yawancin cututtukan da suka shafi ciki.

Ciwon Olsa:


Ganyen Gwaba yana ƙunshi sinadarai masu kawar da Cutar Olsa da kuma saurin warkar da ita ga wa’yanda suka kamu da ita. A yawaita shan shayin ganyen Gwaba.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

 1. AYUBA says

  wani ganye ne ke maganin olsa?

  1. alummarhausa says

   Ka duba wannan Link ɗin

   Maganin Olsa

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »