Tarihin Marigayi Manjo Bulama Biu Jihar Borno.

0 548

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Manjo Bulama Biu shine Babban Jami’in Soja na farko da yasamu haro na Rejimental Sajan Major.

An haifi Maj Bulama Biu a ranar 15 ga watan Maris shekarar alif 1934 a garin Biu, dake jihar Borno a yanzu. Bayan kammala karatunsa na firamare, ya shiga makarantar sakandire.

Ya fara aikin soja ne a ranar 5 ga watan Fabrairu, shekarar alif 1952 lokacin da aka shigar da shi aikin soja. An horar da shi a Kaduna kuma ya yi aiki a Rundunar Sojojin Yammacin Afirka wato (RWAFF).

Lokacin da Sarauniya Elizabeth ta biyu ta ziyarci Najeriya, ta ba shi mukamin Kofur domin shi ne matashin sojan da ya fi kowa ado a faretin da akai.

Bulama ya kasance kofur ne a bataliya ta 44 dake Kaduna a lokacin da ake gudanar da atisayen bataliyar wato (range). Ya zama mafi ƙwarewa a gabaɗaya sojojin da suka halarci wannan atisayen. Hakan ya ba shi karin girma zuwa mukamin Sajan.

Nasarar aikin da ya yi a Kongo don ceto wani jami’in Birtaniya ya ba shi karin girma zuwa mukamin Staff Sajan

Kwazonsa da ƙwarewa na aiki sun bayyana a fili har aka nada shi, a shekarar alif 1964 a matsayin Babban Rejimentar Sajan Major (RSM) na Makarantar Tsaro ta Najeriya.

Ya horar da manyan jami’an sojojin tun daga course 1 zuwa 21.

Domin kwazonsa da hazaƙarasa na aiki a Kwalejin, an ba shi mukamin Kyaftin, sannan aka kai shi makarantar horar da sojoji ta Depot Nigeria Zariya a shekarar alif 1977. Ya zama jami’in kula da Makarantar fareti (Drill) ta Najeriya.

Domin nuna sadaukarwar da ya yi wa kasa, Kyaftin Bulama Biu ya samu lambar yabo ta kasa ta member of the order of Niger, wato (MON) a shekarar alif 1982 wanda shugaban Najeriya na lokacin Alhaji Shehu Shagari ya ba shi.

An kara masa girma zuwa matsayin Manjo sannan aka mayar da shi Makarantar Sojojin Najeriya (NASI) dake Jaji Kaduna a matsayin Kwamanda mai kula da Fareti (Drill).

Ya samu lambar yabo na Sojoji da yawa da suka hada da Medal Independence Nigeria, Medal Kongo, Medal Civil War, Long Service da Good Conduct ta Sarauniya Elizabeth II da Memba na Order of Niger (MON).

Maj Biu ya yi ritaya daga aikin soja a shekarar alif 1987 a matsayin Manjo bayan ya yi hidima na tsawon shekaru talatin da takwas (38).

Aikin da ya yi na karshe shi ne a Makarantar Sojojin Najeriya Jaji shi ne Babban Kwamanda na makarantar Fareti (Drill).

Ya rasu a asibitin koyarwa na Maiduguri a ranar 16 ga watan Maris shekarar alif 1998 bayan ya sha fama da jinya.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »