Yadda Zaa Magance Cutar Shawara Da Typhoid

0 7,129

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Cutar shawara cuta ce wacce kusan dukkan mutanan wannan zamani ana dauke da ita, cut ace wacce idan tayi yawa a jikin mutun take haifar da cutar Taifod (Typhoid), wanda a halin yanzu keda wahalar warkewa a jikin mu.

A wannan bayani da zamuyi  Idan har kana da matsalar cutar Shawara ko Taifod (Typhoid) a cikin jininka, kuma wacce kayi maganin amma ta ki rabuwa da kai to ga  wani magani sai a jarraba shi kozai karbeka.

Abubuwan da zaka nema basu da wahala samu sune kamar haka:

 Ganyen Darbejiya/Dogon yaro/Maina

Abarba ( Babba)

Lemon Grass (NA’A NA’A)

Tsamiya ( KAMAR 2)

Citta ( yar kadan)

Tafarnuwa (KADAN)

Sai a samu tsaftataccen robar ruwa ko gorar ruwa.

Yanda Za’a Hada Maganin:

Bayan ka samo duk abubuwan nan guda 6 da aka lissafa sai kuma ka wanke su sosai, sai ka fere bawan Abarbar ka sanya ta a cikin wankakkiyar karamar tukunya sai ka kara ruwa mai kyau dai dai gwargwado a ciki tare da ganyen Darbejiyar da kuma lemon grass sai ka tafasa su su kai mintuna 30 a wuta.

A gefe daya kuma sai ka bare tafarnuwar, tsamiya da Cittar sai ka markade su, sai ka bari shi wancan ruwan abarbar da na Darbejiyar  yayi sanyi tukunna sai kazo ka hade su wuri daya da markadaddun tafarnuwar, ka sanya su a cikin robar ruwa ka ajiye su a wuri mai sanyi sai ka rika sha kofi 1 safe kafin kaci abinci da kuma dare bayan ka ci abinci.

Allah yabada lafiya daga

Rismawy (Abu Nu’aym)

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »