Tamim Yahuza Shaban wanda aka fi sani da TY Shaban ko Shaba, mawaƙi ne a Najeriya, kuma ɗan wasan kwaikwayo, ɗan rawa, Mai gabatar da shirin TV kuma mai shirya fim a masana’antar shirya fina -finan Hausa wato Kannywood.
An haifi jarumi Shaban ranar 4 ga watan Fabrairu shekarar alif 1980 a yankin Nassarawa dake karamar hukumar Nasarawa a jihar Kano, Najeriya.
Yayi karatunsa na Firamare a Nassarawa Brigade, Sannan yayi karatunsa na Junior Secondary a Kwalejin Malamai ta jihar Kano, sai kuma ya halarci Sakandaren Gwamnati dake Duka a jihar Kano.
Ya yi karatun Noma a Kwalejin Ilimi ta Tarayya dake Bichi (Federal College Of Education Bichi). Ya kuma yi karatun Public Administration a Kano Polytechnic. Ya kuma yi Diploma a fannin shirya fina-finai a Jami’ar Yusuf Maitama Sule, Kano, duk a Jihar Kano.
Jarumi TY Shaban mawaƙi ne kuma mai shirya fina -finai kuma furodusa a masana’antar shirya finafinai ta Kano wato Kannywood.
TY Shaban shine mahaifi ga Sani TY Shaban (Freiiboi) mawakin Hausa HIP-HOP mai shekaru 16 daga Arewa. Shaban ya ce ya sanya dansa cikin filin nishadi ne saboda gano hazaƙar yaron ta fanin waƙa.

An fara sanin Jarumin ne a fagen Mawakan Hausa. Wakokinsa “Uwargida Ran Gida” da kuma “Shaba zo Taho” sun samu karɓuwa kasancewar shigarsu kowane bangare na kasar Hausa.