Tarihin Abba Kabir Yusuf (Abba Gida Gida)

0 3,004

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Abba Kabir Yusuf wanda aka fi sani da Abba Gida Gida an haife shi a ranar 5 ga watan  Janairun shekarar alif 1963, kuma ɗan siyasan Najeriya ne wanda ya tsaya takarar Gwamnan Jihar Kano a zaɓen 2019 a ƙarƙashin Jam’iyyar Demokraɗiyya ta PDP. Haka kuma Suruki ne ga Dr. Rabiu Musa Kwankwaso Abba yayi aiki a majalisar zartarwa ta jihar Kano tun daga daga shekarar 2011 zuwa ta 2015.

Abba ibn Muhammadu Kabir ibn Danmakwayon Kano Yusuf ibn Muhammad Bashir ibn Galadiman Kano Yusuf ibn Sarkin Kano Abdullahi Maje Karofi ibn Sarkin Kano Ibrahim Dabo yana daga ɓangaren Sullubawa Fulani, a bangaren uwa yana da alaka da Walin Zazzau Sheikh Umarul Wali ibn Galadiman  Zazzau Malam Ahmadu, kakan mahaifinsa Zainab ibna Malam Saidu Limamin Huggalawa daga dangin Limamin Huggalawa ne a Bichi, kakar mahaifiyarsa Kahadijatul Naja’atu tana da alaka da Gwani Mukhtar wanda shi ne jagoran Jihadin Fulani a Daular Kanem-Bornu.

abba kabir yusuf
Abba Gida Gida

An haifi Abba Gida Gida a karamar hukumar Gaya ta jihar Kano, dake Najeriya.  Ya tafi makarantar firamare ta Sumaila daga baya kuma ya shiga makarantar sakandaren gwamnati ta Lautai, a ƙaramar hukumar Gumel (yanzu da take  jihar Jigawa), inda ya mallaki takardar shaidar kammala karatu na  farko a shekarar alif 1980. Daga baya, ya samu shiga Federal Polytechnic, Mubi, inda ya samu  Difloma ta kasa a aikin injiniya wato (National Diploma in Civil Engineering) a shekarar alif 1985.

 Daga baya ya sami babbar difloma ta kasa wato (HND) a injiniya, da takardar shaida da ƙwarewa kan albarkatun ruwa/injiniyan muhalli a shekarar alif 1989 daga Kwalejin Kimiyya ta Kaduna, ya yi hidimar Bautar Ƙasa a Hukumar Kare Muhalli ta Kaduna daga shekarar alif 1989 zuwa ta 1990. Sannan yayi karatun postgraduate a fannin gudanarwa, sannan ya sami digiri na biyu a fannin kasuwanci daga Jami’ar Bayero Kano.

Abba ya kasance Kwamishinan Ma’aikatar Ayyuka, Gidaje da Sufuri a Jihar Kano, Abba ya tsaya takara a zaben gwamna  da aka gudanar a shekarar  2019, kuma gwamnan jihar Kano na yanzu Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya kayar da shi.

Abba Gida Gida tare da mai gidansa Dr. Rabiu Musa Kwankwaso sun kai karar zuwa kotu don neman kansa a matsayin zababben gwamna, bayan gudanar da ƙarar, kotun ta yi watsi da karar.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »