Takaitaccen tarihin Jaruma Ummi Rahab

1 4,015

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Jaruma Ummi Rahab na ɗaya daga cikin ƴan mata masu ƙananan shekaru a masana’antar kannywood, ta fara harkan fim tun tana ƙasa da shekaru goma, jarumin kannywood (ADAM A ZANGO) ne ya shigar da ita cikin masana’antar fim. Inda aka fara haskata a fim ɗin jarumin mai suna “Kin Zamo Takwara Ummi “

An haifi Ummi Rahab a ranar 7 ga watan Afrilu na shekarar alif 2003 a Jihar Kaduna. Jarumar ta yi firamare da sakandire duk a jihar Kaduna. A yanzu haka tana zaune a jihar Kano don sana’ar wasan kwaikwayo.

Ummi Rahab

Fim din da ya haskaka jarumar shi ne fim ɗin “Kin Zamo Takwara Ummi”. Inda ta fito a ƴar gidan jarumi Adam A Zango.

Jarumar ta kasance ƙarama. Amma ta sami damar nuna cewa zata iya wasan kwaikwayo. Tun daga nan kyakkyawar jarumar ta zama sananna a masana’antar, a tsakanin tsofaffi da kuma matasa. Bayan wasu shekaru tabar masana’antar don cigaba da karatun ta na Sakandire.

Ummi ta dawo masana’antar tana da shekaru 18 a duniya. Jarumar ta dawo gabaɗaya don ci gaba da sana’arta ta fim. A wannan karon, Ummi ta ƙara girma kuma tauraron ta na haskawa a masana’antar.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

  1. […] post Takaitaccen tarihin Jaruma Ummi Rahab appeared first on Alummar […]

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »