Tarihin Sanata Kabiru Ibrahim Gaya

0 1,442

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

HAIHUWAR SA

An haifi Kabiru Ibrahim Gaya a ranar 16 ga watan Yunin Shekarar alif 1952, ɗan siyasa ne shi a Najeriya kuma magini (architect) ne, wanda aka zaɓe shi zuwa Majalisar Dattawan Najeriya ta Kasa a shekarar 2007, yana wakiltar mazabar Kano ta Kudu a Jihar Kano ƙarƙashin Jam’iyar All Progressive Congress (APC).

MAKARANTAR DA YAYI

Kabiru Ibrahim Gaya yayi makarantar firamare ta Gaya daga shekarar alif 1961 zuwa 1964 da kuma Tsangaya Primary School inda a nan ya gama firamare dinsa a shekarar alif 1968, babban wansa shi ne Shugaban makarantar a wannan lokacin sannan Abdullahi Aliyu Sumaila shi ne Mataimakin Shugaban makaranta wanda ya koya masa ilimin lissafi. a makarantar firamare.

Yayi Makarantar Sakandaren Gwamnati ta Birnin Kudu daga shekarar alif 1969 zuwa 1973 inda ya sami Takaddar Makarantar Afirka ta Yamma wato (WASC) da kuma Kwalejin Nazain daga shekarar alif 1974 zuwa 1975 inda ya sami IJMB.

Kabiru ibrahim Gaya

Ya sami takardar BSc. a Gine-gine daga Jami’ar Ahmadu Bello a shekarar alif 1977. Ya samu digiri na biyu a fannin Kimiyyar kere-kere daga Jami’ar Ahmadu Bello a Shekarar alif 1980.

An ba shi digirin girmamawa a Jami’ar Kimiyya da Aiwatar da Gudanarwa, Porto-Novo, Benin. Ya kasance memba na Cibiyar Nazarin Gine-ginen Najeriya (NIA) da kuma ƙungiyar Manoma (NLSFA).

GWAGWARMAYA

Yana daga cikin memba na KASEPPA a shekarar alif 1985, kuma memba na Kwamitin Kula da Kasa na United Nigeria Congress Party (UNCP). Ya kasance Gwamnan, Jihar Kano a shekarar alif 1992–1993. A shekarar 2003, Kabiru Ibrahim Gaya ya tsaya takara a NDP a zaben fidda gwanin gwamna a jihar Kano.

An zabi Kabiru Gaya a majalisar dattijai mai wakiltar Kano ta Kudu a shekarar 2007. An naɗa shi ɗaya daga cikin kwamitocin Gas, Foreign Debts, States & Local Governmenti, da Albarkatun Man Fetur da Ayyuka. A cikin tsaka-tsakin aikin tantance ayyukan Sanatoci,

A watan Nuwamban shekarar 2009 ne ya goyi bayan kudirin da jam’iyyar ANPP reshen Kano ta yi na ba gwamnan jihar, Ibrahim Shekarau, damar gabatar da dan takarar ANPP a zaben gwamna na 2011. Wanda aka zaba shine Sheikh Ibrahim Khaleel. Kabiru Gaya ya tsaya takarar sanatan Kano ta Kudu a karkashin inuwar jam’iyyar ANPP a watan Afrilun 2011, kuma aka sake zabarsa.

Kabiru Gaya shi ne Mataimakin bulala mara rinjaye na Majalisar Dattawa daga shekarar 2007 har zuwa 2011.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »